Videos

Rikicin Maryam Yahaya da mai shadda akan Auren Hassana Muhammad

Tun dai jarumin Bashir mai shadda yayi aure shikenan aka dinga jin kananun maganganu suna fitowa daga bakin wasu daga cikin jaruman kannywood da suke nuna kishin su a fili wanda hakan yasa jama’a suka zuba ido suga me zai faru

Ana ganin dai kamar Bashir mai shadda ya yaudari yan mata da yawa acikin masana’antar kannywood wa’yanda yanzu duk suka fito suna fadawa duniya cewa ga yaudaresu kuma daga baya yazo ya auri wata wacce basu taba tunani ba

Sai dai jaruma Maryam Yahaya ana ganin kamar abin yafi damunta tunda itace wacce ta fito tana fadawa duniya yadda jarumin ya yaudareta kuma tace bazata yafe ba

Babban abinda ya kara tunzura jarumai mata shine yadda bikin yayi armashi wanda akaga mawaki rarara yayiwa amaryar kyautar damkarereyar mota ƙurar Honda wanda suke ji dama sune aka yiwa wannan kyautar bayan murnar aure sai ga murnar kyautar mota

Wasu sunyi namijin kokari wajen boye soyayyar jarumin yayin da wasu kuma suka kasa hakuri sai da suka bayyana bakin cikinsu afili wanda hakan ba daidai bane

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button