LABARAI/NEWS

Rundunar Ƴansandan Najeriya Ta Haramta Amfani Da SPY Plate Number….

Rundunar Ƴansandan Najeriya Ta Haramta Amfani Da SPY Plate Number….

A wata sanarwa da Magana da yawun Rundunar Ƴansandan CSP OLUMUYIWA ADEJOBI ya sanyama hannu mai taken “Tsaron cikin gida Sufeto Janaral Usman Alkali Baba ya haramta amfani da Lambar da take ɗauke da sunan SPY a faɗin ƙasar nan baki ɗaya.

Sanarwar ta ƙara da cewa Sufeton Ƴansandan ya bada Umarnin ƙwace duk wata lamba da take ɗauke da sunan SPY babu wane ko wanene aka ganshi da ita daga yanzu za’a ƙwace ta, kuma an soke lasisin amfani da Lambar har illa ma Shaa Allah.

Wannan dokar an sanya ta dole ne saboda masu amfani da wannan Lambar suna amfani da ita wajen karya dokokin tuƙi da sauran dokokin ƙasa da dama suna ɓoyewa akan wannan damar da suka samu wajen keta doka.

Sufeto Janaral ya Umarci duk wani Jami’in Ɗan Sanda da yake aiki da manyan Jami’in Gwamnati ya tabbar da anyi amfani da wannan dokar kazalika sauran Jami’an tsaro suma su tabbatar da anbi wannan dokar, yace duk wanda baibi wannan dokar ba Hukuma zata chafke shi.

Haka nan kuma Sanarwar ta ƙara da cewa ƙwamishinonin Ƴansanda Talatin da Shidda na faɗin ƙasar nan da kuma Abuja kazalika Mataimakan Sufeto Janaral da suke kula da shiyyoyin ƙasar nan su tabbar da anbi wannan dokar an kuma ƙwace duk wata lamba ta SPY da yanzu ake amfani da ita.

Ya ƙara da cewa Jami’an tsaro kar su kama kowa wanda yake amfani da wannan Lambar in ba Jami’in Ɗan Sanda bane, ma’ana Wanda yaƙi bin dokar za’a ƙwace Lambar ne kawai a barshi ya kama gaban shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button