LABARAI/NEWS

Rundunar Sojin Najeriya Tana Kara Himma Wajen Horas Da Jami’anta

Rundunar Sojin Najeriya Tana Kara Himma Wajen Horas Da Jami’anta

Rundunar sojin Najeriya ta ce tana aiki tukuru wajen bin umurnin shugaban kasa na kawar da ayyukan yan ta’adda a ko ina cikin fadin kasar.

Daga cikin matakan da take dauka akwai horas da jami’anta inda yanzu haka jami’an da kw matakin saje Manjo ke kan karbar horo.

 

 

Yadda matsalar rashin tsaro ta addabi Najeriya abu ne mai sosa rai wanda ya tayar da hankulan jama’a da dama kuma baya rasa nasaba da dalilin da ya sa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi ta baiwa jami’an tsaro umurni lokuta daban-daban na magance matsalolin tsaro.

Bisa ga umurnin da ya yi ta bayarwa da kuma goyon baya da yake baiwa rundunar sojin kasar babban hafsan mayakan kasa Lt, Gen Faruk Yahaya yace rundunar ta mayar da himma wajen horas da jami’anta tare da samar da ingantattun kayan aiki da ke taimakawa wajen samun nasara.

Yace kuna gani muna samun nasara don dole mu godewa shugaban kasa da kwarin gwuiwa da yake bamu wanda ke kara mana azama yanzu yan ta’adda sun shiga taitayinzu yanzu da barayin daji da yan ta’adda da masu garkuwa da mutane basu da maboya domin muna tafe kansu don aiwatar da dokar shugaban kasa ta kawar da su.

Daga cikin matakan da rundunar ke dauka yanzu haka tana kan horas da jami’anta na Saje Manjo wadanda ake kira RSM wanda shine horaswa karo na biyu a wannan shekara dake gudana a Sakkwato dake arewa maso yammacin kasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button