LABARAI/NEWS

Rundunar yan sandan Kano tace ashe ba tukunyar gas bace ta fashe a Kano sinadaren “Bomb ne”

Rundunar yan sandan Kano tace ashe ba tukunyar gas bace ta fashe a Kano sinadaren “Bomb ne”

…Wanda ke da hannu ya mutu a fashewar

Daga Muryoyi

Fashewar ta jawo mutuwar akalla mutum Tara da kuma raunata wasu da dama.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a ranar Asabar 21 ga watan Mayu, 2022, rundunar ta ce mutumin da yake gudanar da haramtaccen kasuwancin na sayar da wadannan haramtattun sinadarai, wadanda ake hada bam da su, da aka gano, Michael Adejo, ya mutu shima a fashewar.

Sauran wadanda suka mutu tare dashi a cewar Yan-sandan akwai Ejike Vincent (mai walda) da Michael Adejo (mai sayar da sinadarai) da Musa Kalla (mai sayar da shayi da Christiana Abosade da Mary da Austine Dada da Madam Owoleke da Omo Ben da kuma Bose Oladapo.

Rundunar ta kuma bayyana wasu tarin durum-durum da jarkoki da ke dauke da sinadarai iri daban-daban, masu hadari da ta ce ta gano a inda lamarin ya faru.

Tuni dai aka soma kame kan wannan lamari bayan yan sandan sun samu karin hujjoji. Ko a shekaran jiya ma sai da aka kama wata mota makare da sinadaren hada Bom da kuma bindigogi za a shiga dasu Kano

Me zaku ce?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button