ylliX - Online Advertising Network Russia ta sace Daraktan Masana’antar Nukiliyar Ukraine - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Russia ta sace Daraktan Masana’antar Nukiliyar Ukraine

Russia ta sace Daraktan Masana’antar Nukiliyar Ukraine

Sojojin Russia sun yi awon gaba da wani Dakarta-Janar da ke aiki a masana’antar nukiliyarta ta Zaporizhzhia.

Gwamnatin Ukraine na zargin dakarun Russia da azabtarwa da kuma wulakanta babban jam’in a masana’natar nukiliyar da ke yakin Kudancin Ukraine da ke karkashin ikon sojojin Rasha.

Sojojin Russia sun yi gakuwa da Mataimakin Darakta-Janar na Sashen Kula da Ma’aikta a Masana’antar Nukiliya ta Zaporizhzhia, Valeriy Martyniuk,” in ji sanarwar da gwamnatin Ukraine ta fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta yi kira ga Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Grossi da zai kai ziyara Rasha da ya sa baki Rasha ta sako jami’in.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button