ylliX - Online Advertising Network Sabon damfara ga masu POS da ya shigo garin zariya ta hanyar fasa ɗanyen ƙwai. - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Sabon damfara ga masu POS da ya shigo garin zariya ta hanyar fasa ɗanyen ƙwai.

Sabon damfara ga masu POS da ya shigo garin zariya ta hanyar fasa ɗanyen ƙwai.

wani sabon al’amari na damfara da ya bayyana a cikin birnin Zariya. Wanda ba’a san ko iya nan ne yake faruwa ko kuma yana faruwa a sauran wurare ba.

“Kimanin kwanaki uku kenan, wasu mutane su biyu zuwa uku, suke yawo tsakanin unguwar Tukur-Tukur zuwa tudun Wadan zariya, suna damfarar masu sana’ar POS. Waɗannan mutane da ba’a san ko su waye ba kuma ba’a san daga ina suke ba, suna yawo wuraren masu sana’ar POS kaɗai, da sunan cirewa ko tura kuɗi daga bisani sai su damfari masu POS ɗin.

 

 

“Wato abinda suke yi shine, suna zuwa da ƙwai ko kuma lemon roba kodai wani abu mai kama da hakan, wanda idan aka sake shi ya faɗi ko kuma aka buɗe a ture zai zube. Yayin da mai POS yake ƙoƙarin sallamar su sai su zubda wannan abu.

Daga idan mai POS yayi yunƙurin kwashewa kodai ya taɓa, to zai fita daga cikin hayyacin sa. Su kuma zasu ɗibi abinda suke so, wani ma da hannun sa zai ɗibi kuɗi yabasu.

“Da haka ake kira ga al’umma da su yi hattara domin kaucewa faɗama waɗannan azzalumai. Duk inda mai sana’ar POS yaga anyi masa haka toh kada ya taɓa wannan abin da aka Zubar a shagon sa

Yayi kokarin umartan wanda ya zubar ya kwashe abinsa ko kuma ya haɗa su da hukuma idan akwai a kusa.”

A kan cigaba da wannan damfarar da ya ke shirin zama wutar goguwa a cikin birnin Zariya, lallai an tabbatar mana cewa Ƴan damfarar sun iya yin Nasara akan wasu masu sana’ar POS ɗin, “inda suka yi masu awon gaba da maƙidan kuɗaɗe.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button