LABARAI/NEWS
Sabon Kuɗi Naira da aka fito dashi Jabune, Cewar Dr. Ahmad Gumi

Sabon Kuɗi Naira da aka fito dashi Jabune, Cewar Dr. Ahmad Gumi
Fitaccen Malamin Addinin Islama Dr Ahmad Gumi Yace Abinda Ke Faruwa a Cikin Babban Bankin Nigeria Yayi Kama Da Aikin Masu Garkuwa Da Mutane
Babban malamin ya nuna rashin amincewarsu don gane da sabbin kudin da aka fitar ya ce sunfi kama da na bogi kuma wanna ma na da alaƙa da ta’addanci
Shehin Malamin yace yanzu Satar kuɗin da akeyi a CBN Shima Harkan ta’addanci ne babban ta’addanci da yafi na masu garkuwa da mutane
Daktan ya bayyana hakanne a cikin wani Faifan Bidiyo da aka haska yana bayani bayan ya shigo da shi yana tsaka da Wa’azi acikin Masallaci na Sultan Bello Kaduna