Nishadi

Safarau ta gindaya tsauraran sharuda ga wanda suke son auren ta

Safarau ta zayyana wasu sharuda ga duk wanda yake don auren ta lamarin da ya haifar da Cece kuce a kafafen sada zumunta

 

 

Fitacciyar jaruma kuma mawaki safarau ta bayyana hakan ne a bayan da ta ke yawan samun sakonni daga mutane da dama ba don auren ta

 

 

Duk da cewa jarumar a baya ta sha matukar suka kan wani fefan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta wanda ya nuna tsaraicin jarumar

 

 

Sharudan da safarau ta bayyana ya hadar da cewa dole ne duk wanda ya ke son ta ya barta ta cigaba da yin waka ko kuma ya bata harin Naira miliyan dari

 

 

Dole ne duk wanda yake don auren ta ya siya mata mota ta kimanin kudi Naira miliyan biyar zuwa sama da kuma katafaran gidan kwauta

 

 

Wannan na daya daga cikin wasu daga cikin sharuddan da safarau ta bayyana ga duk wanda yake son auren ta inda ta nemi duk wanda ya san zai iya cika wannan sharadi na ta toh tana maraba da shi

 

 

Wannan sharuda ya janyo Cece kuce mai zafin gaske musamman a kafar sada zumunta inda mutane ke cigaba da fadin albarkacin bakin su kan wannan batu

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button