Latest Hausa Novels

SAHIHIN BAYANI GAME DA CIWON ƘODA [KIDNEY DISEASE]

SAHIHIN BAYANI GAME DA CIWON ƘODA [KIDNEY DISEASE]
┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

Hakika muna wani zamani a yanzu da kusan cuttuka kullum kara ɓarko kai suke tare da bijirewa magunguna. Wasu kuma ana warkewa amma ana daukar tsawon lokaci ana fama. Wasu kuma haka za’aita fama da magani har tsawon rayuwa!

CIWON ƘODA (kidney disease) yana daya daga cikin cuttukan da sukai fice a wannan lokaci namu don haka na zabi na kara wayar muna dakai akansa duk da nasha yin bayanin abaya, amma tunasarwa abace mai mahimmanci.

A jikin dan Adam ubangiji ya yimu da k’oda wato (kidney) domin mahimman abubuwa wanda suka kunshi:

■ Samar da sabbin sinadaran kwayoyin jini.

■ Tace jini tare da fitar da gurbataccen abunda muka ci wanda jiki baya bukata

■ Tacewa tare da Samar da fitsari

■ Samar da sinadarin da zai taimakawa kasusuwan jikin mu sui qarko.

■ Taimakawa wajen saisaitawa da sarrafa sugar ajikin mu domin samun kuzari

■ Taimakawa wajen rage zafin karfin tafiyar jinin da zuciyar mu ke bugowa zuwa sauran sassan jiki, wanda daba dan haka ba kowa sai ya sami hawan jini

■ Fitar da abunda jiki bayaso zuwa ga bahaya wato (nitrogenous waste). Dadai sauran su.

WANNAN YASA

Kowanne dan Adam yake da kodoji guda biyu a jika kowane mutum ta hagu da kuma ta dama, wadanda keda mazauni a kwi6i ko gefen ciki karkashin hakarkari ta baya (retroperitoneal), Saboda in daya ta gaza dayar zata taimaka tai aikin. Babu wani mutum a halitta me kidney guda daya gaskiya, saide in mutum an haifosa da nakasa wato koda biyu ahade da juna wato (Horse shoe) wanda da yawa wannan ke kashesu basa tasawon rai ma..

Kasancewarta biyu ko shyasa wani saita sami matsalama ta warkar da kanta batare da ya sani bi kamar a hatsari na kunan wuta, ko amai da gudawa yawanci takan ta6u.

Duba da mazauninta wato baya ne kadai ake iya ganinta ba kamar sauran kayan ciki ba da ake gani ta gaba zarar ta sami matsala ta bangaren data ta6u tanan ake fara Jin ciwon baya me zafi saboda sun gogar tsokar gadon baya (Quadratus lumborum) da suke kwance akanta,

Sannan daga jikinsu wata magudanar fitsari ce da ake Kira (ureter) ta sauko ta hadu da tantanin tara fitsari dake mara wato (bladder).

Ta wannan bututun mahada fitsari kan gangaro ya taru a mara kafin mutum ya fitsarar dashi ta mafitsara wato (urethra).

Ajikin bututun mafitsarar akwai inda tadan tsutstsuke har guri uku duk dan hana fitsari ya komawa kidney yai mata illah, wannan yasa daga kan wannan magudanar fitsari (ureter) zuwa mafitsara (bladder), duk ciwon daya faru a wannan waje kan iya hawa ya ta6a koda.

Kamar yadda na fada abaya koda (kidney) na aiki a matsayin matatar jinin daya kwaso kayan abinci da ruwa ko magani, yabi ta cikinta don atace a samar da fitsari.

Kunga fitsari da jini kenan yana dauke da ruwa da wasu sinadarai da jiki baya bukata, yawancinsu masu guba, kamar gubar ammonia, creatinine, uric acid, urea, nitrogen da sauransu. Idan k’oda ba lafiya, ruwan da ya kamata afitar mai dauke da wannan guba kan taru ajika wanda akan gani a matsayin kumburin jiki (fuska da kafafuwa da hannuwa) a farko-farko kenan kafin daga bisani yabi duk jiki gaba daya (Anasarca).

Kumburin yana da dan bambanci da kumburin ciwon zuciya dana ciwon hanta.

Bayan tace jini, koda tana sarrafa sinadaran bitaman na rukunin D (dake kara kwarin Qashi) da erythropoietin maisa jiki ya kera jajayen ‘ya’yan halittu na jini kamar yadda na fada.

Idan koda nada ciwo mai tsanani bata iya samar da wadannan sinadari wanda hakan kansa jini yayi karanci ajikin mai ciwon, ko karancin sinadarin bitamin D.

A lokuta da dama koda zata iya samun ciwo kuma ta farfado batare da anga alamu ba. Idan har aka fara ganin alamu na kumburin jiki da rashin jini a jiki to sai anyi da gaske kafin a shawo kan ciwon, wanda da yawa kuma maganin shine dashen wata kodar ta daban ko wanke jini da na’ura mai aiki kamar kodar da ake kira dialysis machine akai akai idan aikin kodar bai kasa sosai ba wanda bakaramin kashe kudi ake ba.

Wasu kuma abubuwan wani ne ke tada wani a gwajin wani ciwon akan gano kodar bata aiki yadda ya kamata

Wannan cigaba na dashen koda ko wanke jinin masu cutar da na’ura domin fitar musu da dattin jikin da kodar bata iya fitarwa a yanzu ana iya yinsa a nijeriya, sai dai kwai tsada. Shiyasa yake da kyau asan abubuwan dake kawo ciwon koda ko a dauki matakan kariya. Itade lafiya guda 1 ce kiwonta ake, Inka rasata duk gatanka ka riga ka rasata.

Saide wani batu mai kwantar da hankali game da koda shine aikin da koda biyu suke yi, guda daya ma zata iyayi batare da wata matsala ba ko da mutum ya bada taimakon daya daga ciki ga me bukata. Don haka nema ake ganin wadanda aka ciri daya daga cikin kodarsu aka dasa wa wani kanyi rayuwarsu kamar kowa.

Shyasa kamar yadda na fada babu mutum me koda daya atsarin halitta kamar yadda wasu ke fadi, A’a duk wanda kagani da koda daya to matsala aka samu tun aciki wajen goyon cikinsa abunda ake Kira CONGENITAL ANOMALIES wato (horse shoe) kidney, kamar kofaton doki a manne dake kasancewa dunkule atsakiya amma bawani mutum mai koda daya a normal condition.

🛑
ME KE HADDASA CIWON KODAR

Abubuwan da suke kawo ciwon koda suna da yawa kama daga:

  1. Akwai kurarraji ko bororon koda da ake kira polycystic inda ake ganin kamar wasu kuraje kunshe da ruwa ajikin kodar… wanda shi wannan gadonsa ake.
  2. Wasarairai da cuttukan hawan jini da ciwon suga danansha bayani kansu sune kan gaba wajen sanadin ciwon koda. Don haka inma mutum baisan matsayinsa ba ina baku shawara kuje kui gwaji…. karka dogara da kanajinka lfy baka da alamun komi kace zaka zauna.
  3. Sai shan magunguna ba bisa ka’ida ba musamman ga mata dake shan magungunan ciwon mara kala kala yayin period,
  4. Shan magunguna batare da umarnin likita ba, misali kurum dan mutum yaji ciwon kai sai ya nemi irinsu paracetamol, Aspirin, feldin ko Ibuprofen yasha.
  5. Sai kuma kurakuren kananun ma’aikatan lafiya nayin aikin da banasu ba, a maimakon tura mara lfy ga likitocin da suka dace… wasu na dora mutum Kän magani ko allurai batare da cikakken ilimi ko sani akan yadda maganin karankansa ke aiki ajika tare da toxicity da side effects dinsa ba.
  6. Shan barasa,
  7. Karancin shan ruwa,
  8. Yawan cin nama,
  9. Yawan shan gishiri,
  10. Yawan cin abubuwa masu kitse (junk foods) su chocolate da sauransu

Sauran su ne:-

● Toshewar mafitsara da kwayoyin cuta ke jawowa. Wanda wannan ciwon koda wanda toshewar mafitsara kan jawo Akwai cututtukan da kan toshe wasu daga cikin sassa na mafitsara (tun daga bakin kodar har zuwa wurin fitar fitsarin). Ta yadda Idan hakan ta faru, maimakon fitsari ya zirare, sai ya taru ya kumbura wurin da abin ya faru, daga nan sai yayi sama ya taru a kodar, itama karshe ta kumbura, yadda idan ba a dauki mataki ba, takan mutu gaba daya ahankali ahankali.

Amma da zarar ankawar da abinda ya toshe mafitsarar cikin sauri, sai kodar ta dawo aiki kamar ba abinda ya ta6ata.

Idan toshewar saman tantanin fitsari ce, akan ga bangaren koda gudane ke kamuwa kuma mutum zai iya kamuwa har koda ta tabu bai sani ba.

Amma idan daga kan tantanin zuwa kasa aka samu toshewar, kusan duka koda biyun zasu iya harbuwa.

WADANNE CUTTUKA KAN TSOHE MAFITSARAR

Irin cututtukan da kan toshe mafitsara matsaloli ne irinsu;

-Tsakuwa (stones) da k’ari ko
-Tsuro na tantanin fitsari, da
-Qari na bakin mahaifa da
-Kumburin prostate (a wasu maza
wadanda suka zarta shekaru hamsin).

Da sauran irin wadannan cututtuka masu alamu, duk kusan iri daya, kan kawo cikas ga kwaranyewar fitsari yadda ya kamata, wanda hakan kan taba lafiyar koda.

ALAMOMIN CIWON KODA

Idan saman tantanin mara na fitsari ciwon yake; akan samu;

■ Ciwon kwi6in ciki daga lokaci zuwa lokaci, Wani zubin harda yunkurin amai, koma aman. Wanda Irin wannan tsakuwa ce tafi kawo shi kuma ciwon kwi6in yafi tsanani, don har kwantar da mutum zai iya yi, mutum ya kasa katabus.

■ Idan kuma daga mara ne zuwa kasa ciwon yake, za a ji ciwon mara maimakon na kwi6in ciki, ko arika fitsari da jini da jin zafi da wahalar fitar fitsari, ko aga fitsari na rabuwa biyu (a maza)

■ Jin dandanon kamar karfe me tsatsa abaki. Matukar ba a mata masu ciki ba.

■ Yawan gajiya, Ciwon kafada, da karanci ko sarkewar numfashi

■ Sai kuraje ajika wanda za’a ga anata magani amma kosun tafi sai su dawo, saboda ba ainishin matsalar Akai magani ba.

🛑
HANYOYIN DA ZA’A KARE KAI

1]- Duk me hawan jini ko ciwon kar yai wasa ko daga kafa wajen shan magani. Sannan wajibi ya kiyaye abubuwan da aja hanashi ci don tattalin lafiyarsa. Taurin kai ba naku bane komi sonku da abun kuwa. Haka duk wanda yasan yana fama da wani yanayi da yasa kullum sai ya sha magani shima ya maida hankali tare da mu’amalantar likitansa da bibiyarsa akai akai.

2] Duk wanda aka taba samun a danginsa ancire wa wani tsakuwa a kodarsa (kidney stones) ko a matsarmama (gallstones), to shima yana cikin hadarin samun tsakuwa a koda.

3]- Akwai abinci kuma irinsu alayyahu da jan nama, wadanda sukan jawo saurin samun taruwar uric acid dake haifar da tsakuwa a koda, don haka wadannan mutane ya kamata su nisance su amma da hujjar zasu maye gurbin abincin da wani irinsa, kamar latas da kifi a wadanda suke da high uric acid level… musamman masu ciwon suga.

4] Haka yawan shan sinadri ko abincin da ya kunshi calcium musamman irin masu yawan shan madarar nan ba tare da kuna wani motsa jikin kirki ba hakan na jawo tsakuwa. Ba dadi bane wuya kuke shama kanku

5]- Akwai kuma yanayi na zafi da kan iya sa taruwar ita wannan tsakuwa, duka dai a irin wadannan mutane da kan iya samu. Don haka yawan shan ruwa lokutan zafi yakan kiyaye taruwar dattin da zasu hadu su bada tsakuwa.

6]- Ga masu noman rani na fadama, ko na damina a gonar da ruwa kan taru, ba tare da sun sa takalmin ruwa ba, da masu wanka a ruwa maras tsabta kamar kududdufi duk ya kamata susan cewa akwai kwayayen ciwon tsargiya da kan iya shiga jikinsu su kawo kari a tantanin fitsari wanda karshe Kän yi tasiri ga koda.

Don haka takalman roba (takalmin ruwa) ga manoma don kariya daga kwayayen schistosoma zai iya kiyaye su. Su kuma masu wankan rafi ko kududdufi, sai dai su guji hakan, don kuwa suma suna cikin hadarin kamuwa da wannan tsuro.

7]- Duk wanda ya taba noman fadama inda ruwa kan kwanta, ba tare da takalmin ruwa ba, ko kuma ya taba yin wankan rafi, musamman idan mutum ya taba yin tsargiya ko fitsarin jini amma bai sha magani ba har yaga kamar ciwon ya tafi dan kanshi, to yana da kyau yaje asibiti mafi kusa a gwada fitsarinsa a kuma ba shi maganin kashe wadannan tsutsotsi masu kawo tsuro a mafitsara.

80]- Duk namjin da ya taba yin ciwon sanyi, mai alamu na ganin farin ruwa kamar kamu a karshen fitsari, bai je anba shi magungunan da suka dace ba, shima yana cikin hadarin kamuwa da toshewar mafitsara a nan gaba, don haka da zarar an ga irin wannan alamun ciwon sanyin ake daukar mataki kafin abin ya zama matsala musamman masu saduwa da mata barkatai.

9]- Yana da kyau duk macen data kai shekaru arba’in ta rika zuwa asibiti akalla sau daya a shekara ana gwada ruwan bakin mahaifarta wato (pap smear) don kiyaye kamuwa daga ciwon daji na bakin mahaifa. Amma ni ashawarata basai kin kai 40yrs ba at 35years ma yafi.

10]- Duk namijin da ya manyanta, yaba arba’in da biyar baya, kuma yake da wahalar fitar fitsari, ko jinkiri wajen fitsari, shima ya samawa kansa lafiya, yaje yaga likita domin duba prostate dinsa.

11]- Duk mai ciwon kwi6in ciki, na bangare daya ko duk biyun kuma ciwon yaki-ci-yaki cinyewa, to yaje yaga likita ko ayi masa hotunan koda ultrasound wadanda kan iya nuna duk wata matsala a kodar kamar tsakuwa.

12] Karamin ma’aikacin lfy idan kayi iya kokarinka abu yaci tura kai tsaye ka tura mutum zuwa ga babban asibiti inda ake da kwararru hakan ba gajiyawa bane.

13] Ku kiyayi browsing din sunayen magunguna a internet kuna sha Wallahi wasu wannan ke kashe su tsakar dare alhalin ansan lfy aka rabu dasu, haka wannan ma na Kän gaba wajen kashe koda.

14] Dan kawarki ko abokinka yai fama da matsala irin taka ka ya warke ka Guji karbar magani irin wanda aka bashi kace kaima zaka sha, wannan ma na kashe koda. Kaje asibiti likita ya baka da kanshi.

Wannan shine bayanin ahakan ma gaskiya takaitawa nayi, nasan bayanin yai tsayi amma Inkuka rike kuka ilmantu ko kuka samu littafi kuka rubuta zai amfaneku ko ya’yanku koda bama raye.

Allah ka kara muna lafiya amin!!!

[I. Y. YUSUF]

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button