Sallah a kasuwa ta janyowa wata yar tallan kabakin arziki na kayan daki

Rikon sallah ta kawowa wata mai talla kwanakin arziki inda aka gwangwaje ta da sababbin kayan daki
Mai talla dai an dauke ta hoto ne a dai dai lokacin da take yin Sallah a cikin kasuwar kafar ruwa da ke jihar Kano lamarin da ya jawo mata kabakin arziki
Abdulkarim wanda shine ta dauki hoton nata lokacin da take sallah tare da wallafawa a kafar facebook ya nuna matukar farin cikin sa kan wannan kabakin arziki da yar Talakan ta samu
Wannan dai babban darasi ne ga duk wasu masu talla haka zalika darasi ga duk masu wasa da sallah
Wanna kabakin arziki da yar tallan ta samu ta zamo abin fada a shafukan yanar gizo dama na sada zumunta inda ake ta aikewa da yar talla da murna da kuma taya ta farin ciki ga banin auren ta