LABARAI/NEWS

Sarauniyar Giwayen Kenya ta mutu tana da shekara 65

Sarauniyar Giwayen Kenya ta mutu tana da shekara 65

Masu kula da gandun daji a kasar Kenya na makokin mutuwar fitacciyar giwar kasar da aka fi sani da ‘Sarauniyar’ giwayen kasar tana da shekara 65 a gandun dajin Tsavo da ke gabashin kasar.

Hukumar kula da namun dajin kasar ta ce giwar ta mutu ne sakamakon yawan shekaru Tsohuwar giwar – mai suna Dida wadda kuma aka fi sani da ‘Sarauniyar giwaye’ – ta sha tsallake kalubale da dama a kasar kamar farin da kasar ke fuskanta.

A wasu jerin sakonni da ma’aikatan gandun dajin kasar suka yi ta wallafawa a shafukansu na Tuwita, sun bayyana kaduwa da alhininsu bayan mutuwar sarauniyar Giwayen

Gandun dajin ya bayyana Dida a matsayin giwar da gandun dajin ba zai taba mantawa da ita ba.
Haka kuma an bayar da rahoton mutuwar wasu giwayen biyu a gandun dajin Imenti na kasar.

A ‘yan watannin baya-bayan nan dai ana samun karuwar yawan mace-macen dabbobin dawa, lamarin da ya haddasa mutuwar giwaye sama da 100 a gandun dazukan kasar da daban-daban, kamar yadda gidauniyar kula da namun daji ta Afirka ta bayyana.

Masu kula da gandun dajin na ganin hakan a matsayin wani koma baya ga fannin tattalin arzikin kasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button