SARKIN MUSULMI MASOYIN ANNABI (SAWW) NE.

SARKIN MUSULMI MASOYIN ANNABI (SAWW) NE.
Hakikanin Abinda Ke faruwa na Yadawa cewa, Sarkin Musulmi Ya sa an kama wayanda Suka kashe wacce ta zagi Annabi (Saww), Wannan Karyane, Babu wata hukuma ta ‘yan Sanda ko Jamian Farin Kaya na DSS da Sarkin musulmi yasa ta kama wani.
Haka Kuma yad’a cewa, da Akeyi Sarkin Musulmi yayi Allah waddai da abinda Matasa sukayi Shima wannan Kiren Karyane Ga Sarkin Musulmi.
Domin Lokacin da Wannaan Abin ya faru Mai Alfarma Sarkin Musulmi baya Gari Yana Abuja domin yin Meeting da ASUU game da Yajin aikinsu sai aka kirashi aka gaya mai Cewa, Ga abinda ya faru a Sokoto wata ta zagi Annabi (Saww), kuma har an kasheta, kuma har Jami’an Tsaro sun kama wasu matasa. Shine, Sarki Ya bukaci da ‘yan Majalisa suyi Allah waddai da abinda wannan mata tayi. Sannan ya bukaci Jami’an tsaro da suyi bincike kan lamarin domin yiwa Wayannan Yara Adalci.
Shine aka fitarda wannaan takarda da Turanci, amma mutane suka Kuskure Wannan bayanin.
MATSAYAR SARKIN MUSULMI
Dazu na Kira Mai Alfarma sarkin Musulmi Sai Yace, Jamilu Naji abu na faaruwa a Social Media daga Fitowa ta daga meeting jiya, amma baku ce komai ba, Ku Gayawa Al’umma Cewa, Hakika Mu Masoyan Annabi (Saww) ne, Kuma bamu da Abin Bugun Gaba Kamar Annaabi (Saww). Ammma zamu yiwa Al’umma Bayani.
BAYANI NA NI KUMA
Ina son Al’umma Su kara tabbatarwa cewa, kare Martabar Annabi (Saww) Wajibine, kuma Shine ma Musulunci.
Ranmu da Dukiyarmu Fansane ga Annabi (Saww), Allah ya karawa Annabi Daraja.
Jamilu Sani Rarah Sokoto