Videos

Sati Daya cif Maryam Yahaya tana rakashewa a kasar Dubai

Sati Daya cif Maryam Yahaya tana rakashewa a kasar Dubai

Lallai lamarin wannan jarumar yana bawa mutane mamaki daban al’ajabi saboda yadda aka ga a kullum kara kere sauran yan uwansa jarumai mata take yi gashi nata dade da samun lafiya ba wanda mutane suke mamakin shin a ina wanann jarumar ta samu wannan kudaden da take wannan abubuwan a kasar Larabawa saboda abin yana nema ya fara yawa

Tun sanda wannan jarumar ta cille ta tafi chan kasar hadaddiyar Daular Larabawa wato ƙasar Dubai ba’a kara jin duriyar taba saboda akwai uwar kudin ta ajikinta kunga kuwa sai abinda akaga gani inda Hausawa ke cewa kuturu da kudinsa alkaki saina kasan kwano wanda kamar haka ne a wajen wannan jarumar

Yanzu ana tunanin duk kannywood babu wata jaruma wacce ta taɓa zuwa kasar Dubai tayi wannan adadin lokacin da wannan jarumar tayi wanda hakan ba karamin abin farin ciki bane a waje ta tunda kullum kara samun nasara da cigaba take wajen kere taguwar yan uwanta yan kannywood

Inda wasu kuma na ganin kamar wannan jarumar ba wani kudin kirki take kashewa ba saboda a wajen wa’yanda suka taba zuwa wannan kasar sun riga sun san komai wajen kashe kudi daga wajen cin abinci hatta wajen kwana sunan duka nawa ake kashewa

Sai dai duk da haka masoyan wannan jarumar suna mata kallon a yanzu a kannywood babu wata jaruma wacce zata iya goga kafata da wannan jaruma wato Maryam Yahaya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button