LABARAI/NEWS

Saudiyya ta amincewa Ronaldo yai zaman dadiro da sahibar sa Georgina

Saudiyya ta amincewa Ronaldo yai zaman dadiro da sahibar sa Georgina

Rahotanni daga kasar Saudiyya na nuni da cewa Cristiano Ronaldo da sahibar sa Georgina Rodriguez za su sami takardar izinin zama tare duk kuwa da dokar da ƙasar ta yi mai tsauri a kan zaman dadiro

 

Dan wasan mai shekaru 37 ya koma Al-Nassr ta Saudiyya kan kwantiragin shekara biyu da rabi ta kimanin fam miliyan 173 a kakar wasa bayan kwantiraginsa da Manchester United ta rushe.

 

 

Sai dai kuma zaman Ronaldo tare da Georgina zai kasance karya dokar auratayya a Saudiyya

 

Ronaldo mai ƴaƴa biyar da kuma Georgina wa ce ta haifa masa ƴaƴa biyu za su samu izinin zaman ne duba da cewa ya na ɗaya daga cikin ƴan wasan da suka fi kasuwa a duniya

Rahoton ya ci gaba da ambato wasu lauyoyin Saudiyya biyu wadanda ke hasashen hukumomi ba za su tsoma baki a kan lamarin ba

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button