Saudiyya ta raba kayan tallafi ga waɗanda ta’addanci ya ɗaiɗaita su dubu 16 a Borno

Saudiyya ta raba kayan tallafi ga waɗanda ta’addanci ya ɗaiɗaita su dubu 16 a Borno
Magidanta 16,000 da ke fama da tashe tashen hankula a Borno sun sami tallafin kayan agaji da gwamnatin Saudiyya ta bayar
Tallafin dai shi ne karo na uku da mahukuntan Saudiyya suka bayar ga wadanda rikicin Boko Haram ya shafa a Borno ta hannun cibiyar agajin jin kai ta Sarki Salman
Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ce ta raba kayan tallafin
A sakonsa na rabon kayayyakin da aka gudanar a yau Alhamis a sansanin ƴan gudun hijira na Muna Kumburi Darakta Janar na NEMA Mustafa Habib, ya ce an bayar da irin wannan tallafi ga wadanda abin ya shafa a Yobe da Zamfara
Cibiyar ta ba da gudummawar kayan abinci buhuna 16,000 na kayan agaji ga gidaje 16,000 a jihar Borno don zagaye biyu na gidaje 8,000 kowanne a sansanoni daban-daban a cikin Disamba 2022