ylliX - Online Advertising Network Shari'ar dan China wanda ake zargin da kisan Budurwar sa ummita a jihar Kano - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Shari’ar dan China wanda ake zargin da kisan Budurwar sa ummita a jihar Kano

Shari’ar dan China wanda ake zargin da kisan Budurwar sa ummita a jihar Kano

 

A zaman kotun da akayi a yau, lauyan dan China ya bayyana cewa dan China har garin su, Sakoto yaje sau uku yana gaishe da iya yenta tare da yi musu kyaututtuka , sun kuma shafe shekara biyu tare da Ummita.

Amma mahaifiyar Ummita ta ce sau daya ta san yaje sokoto.

 

Lauyan dan China ya tambayi Kanwar Ummita cewar ko tasan dan China ya kashe wa Ummita kudi miliyan dari da saba’in, ya ce ya kuma saka mata wani tallafi da yake bata dubu dari duk sati , Haka kuma ya taba shirya wa Ummita bikin birthday da a kashe kudi sama da dubu dari bakwai da saba’in.

Ya kuma siya mata gwala-gwalai na sama da naira miliyan uku da dubu dari uku a watan mayu na shekarar da muke ciki.

Sai dai Kanwar Ummita tace bata san ya yiwa Ummita wadannan abubuwan ba kawai tasan ‘yan uwansu ne basa son auren Ummita da dan China.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button