Girki Adon Uwargida

Shawara Ga Ma’aurata (2)

Shawara Ga Ma’aurata (2)

NABEELA IBRAHIM KHALEEL

Assalamu alaikum masoya wannan fili mai fadakarwa a kan abin da ya shafi iyali yau ma ga ni da karashen rubutun da na fara kimanin mako biyu da suka wuce kamar yadda na yi alkawari.

6- Daren Tarewa:

Akwai ladubba da ma’aurata ya kamata su lazumta (aikata) a darensu na farko wato ranar tarewa;

1- Ango zai shiga da sallama tare da addu’ar shiga gida

2- Ango zai shiga da kayan makulashe kamar naman kaza da madara ko nono da kayan itatuwa daidai gwargwadon ikonsa

3- Amarya za ta caba ado tare da feshe jikinta da kayan kamshi don tarbar angonta

4- Za su yi alwala sannan su yi Sallah raka’a biyu sai ya cire kallabinta ya dafa goshinta ya karanta “Allahumma inni as’aluka min khairiha wa khairi ma jabaltaha alaihi, wa a’uzubika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi”.

5- Sai ango ya yi mata nasiha su yi musayar tausasan kalamai na kauna da jaddada rikon amana da kula da tausayin juna da kiyaye hakkokin juna.

6- Addu’ar saduwa:

Annabi (SAW) ya ce “duk wanda ya karanta wannan addu’ar yayin saduwa da iyalinsa Allah Zai tsare abin da aka samu daga Shaidan” ga ta kamar haka: “Allahumma jannibni-shaidana wa jannibib-shaidana ma razakatana”.

7- Tsarki:

Tsarki ya kasu gida uku;

1- Tsarkin zuciya: Mutum ya bauta wa Allah Shi kadai kada ya hada Shi da wani wajen bauta kuma wanin ko wane ne, sannan ya yi koyi da Annabi (SAW) in zai yi ibadar.

2- Tsarkin jiki: Shi ma ya kasu gida biyu, tsarki na jiki wanda mutum zai yi wanka ya caba ado sai tsarki na kari wato mutum ya yi wankan tsarki wanda zan kawo shi nan gaba.

3- Tsarki na wuri: Yadda mace za ta kula da tsabtace muhallinta.

Abin da ya shafi shara, goge dakuna da ruwa, wanke kewaye (bayi) da sauransu.

Akwai matar da in ka leka karkashin gadonta ko kujerunta za ka ga tulin kayan wanki..

 

Please share it for others

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button