Daga Malaman muGirki Adon UwargidaIslamic Chemist

SHAWARA GA MA’AURATA MAZA

SHAWARA GA MA’AURATA MAZA.

ka zamo mutum mai nutsuwa kar ka sake ka rinka aikata abubuwan da zasu jawo maka zubewar mutuncinka a kuma jawo zubewar mutuncin iyalanka kamar shaye-shayen , hakika shaye-shayen yana jawo raguwar kima da kuma yawan alfasha ya kasance ba ka da aiki sai zagi don akwai wadanda zagin ya zama musu Riga ya zame musu jiki, ko zance zasu yi sai sun hada da alfasha kunga ai wannan ba tarbiyar bace ta gari
idan baka so ya’yan ka su dauka sai ka daina.

SHAWARA GA MA’AURATA MATA

kiji tsoron Allah ki kula da mijinki, ki ba shi kulawa ta musamman ki zama mai tsafta da iya ado, ki zamo mai kisisinar da gwalli, da rangwada duk hanyar da Zaki Bi , ta haka Zaki dauke hankalinsa ya daina kula yan’mata da zawarawa a waje. amma kin kasa kula da shi kin kasa kula da kanki, ba ki San me zai ja hankalin mijinki ba, kin zauna daga ke sai dauri iya kirji, ba wankin baki ba gyaran ga shi, ba kula da kafa ba wanki ba wanka ba aski hammatarki bare na gaba ( farji ) dole ki samu matsala don haka ki gyara in kina so ki ga dai-dai.

SHAWARA GA MA’AURATA MATA

Ki zamo mace ta gari ta kwarai ki zamo mai samawa mai gidanki farin ciki karki sa masa tashin hankali da bacin rai karki zagi mijinki karki yi abinda zai bata masa rai

Musamman wajan kwanciya wasu matan suna azabtar da mazajensu ta wannan hanya wata in bai neme taba ba zata Kai kantaba wai ba aji waya gaya miki kyaje wajen Jan ajin matsa sha’awa ko bai niyyar yi ba yaji yana bukarta yayi kuma ta haka hankalinsa zai dawo jikinki ko yaushe yaji yana so ya kasance da ke ki kula garin Neman gira a rasa Ido.

SHAWARA GA MAZA

ka nemi halali ka ciyar da ya’yanka da iyalanka ,ka sa halali ka tufatar da iyalanka da iyayenka da halali, kada kaci haramun ko kasa haramun ko ka ciyar da ya’yanka da iyayenka da haramun, Ku Sani, haramun tana lalata rayuwa , tare da Hana karbar addu’o’in don haka Ku gujewa duk abinda kuka San zai iya jefa Ku cikin fushin ubangiji.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button