Latest Hausa NovelsFadakarwa

SHAWARWARI AKAN KULA DA KODA (KIDNEY) 2022

SAWARWARI AKAN KULA DA KODA (KIDNEY) 2022

Duk kuɗin ka, duk yawan danginka, Duk wani gatan da kake ko kike taƙama dashi! Kuji tsoron gamuwa da cutar ƙoda (kidney disease).

Tun wuri mutum ya kiyayi kansa, yabi matakan kare kai da Masana keta bayani. Sati 1 na iya canza lissafin rayuwarka, komi busy kuke ware lokaci ku riƙa jin me duniya ke ciki a ɓangaren lafiya, da abinda ya kamata kuke yi.

Wallahi duk kokarin ka wannan ciwon yafi ka, sauran batu ku tuntuɓi wani da kuka san ya taɓa jinyar me ciwon kusha labari.

Duk yawan dangin ka sai masu baka gudummawar jini sun gajiya,
duk kudinka koda zaka samu aima dashe saika gama ganin shiga uku, domin dole akwai lalacewar da sai anjira tayi kafin ma aima dashen in ansami me baka, kuma ko anyi babu guarantee.

Kai shi kansa dialysis ɗin mutum kan fita hayyacinsa, yana kuma haddasa mantuwa. Baya ga tarin azaba da ake sha, gashi akalla tun huɗu na dare dole kaje ka kwana a layi kuma sai wani daren kila ka’ida ka sami wankin ƙodar ka koma gida, bayan kwana 3 haka za’a kuma dawowa dakai. Wallahi ko maƙiyi bama masa fata.

Don haka, kaima yanzu haka ta yiwu kana da ciwon, ko kuwa ka taɓa samun ciwon sau ɗaya (acute kidney injury) amma ƙodar ta gyara kanta batare da kasan ma tayi ciwo ba, toh ka guji ta qara samun matsala daga nan bazata warke ba, sau ɗaya ake Mata kuskure ta yafe. Sannan ku kiyayi gishiri koda baku da hawan jini ko ciwon sugar. Duk me ciwon da aka dorasa kan magani ya maida hankali, a kiyayi sayen magani daka ana sha.

Duk wanda akace wankin ƙoda sai an nemi taimako yake samu kai kasan kurum zance ya ƙare.

Wannan shine saƙona gareku a wannan kwanaki da aka ware tun daga jiya 10th March, domin tunawa da masu larurar. Allah ka yaye mana larura da masifa, kai mana maganin abinda bazamu iya ba.

Jumat_Mubarak

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button