Fadakarwa

Shawarwari Ga Sabbin Zaurawa

Shawarwari Ga Sabbin Zaurawa

Amincihausatv.com

Kaman yadda ake aure haka ma ake saki. Wasu lukutan shi wannan sakin suwa kawai yake yi ba tare mace tayi tsammaninsa saboda rashin tasirin abunda ya haddasa saki.
Ga wasu shawarwari da duk wata sabuwar bazawara zata yi amfani dasu domin inganta rayuwarta.

Amincihausatv.com

1: Ki Maida Lamari Ga Allah: Ki sani mutuwar aurenki ba shine tashin alkiyamarki ba. Sau tari wani sakin shine zai zame Miki alheri. Don haka ki tattara lamuranki ki damkawa Allah kada ki zargi kowa akan mutuwar aureki koda kuwa ya bayyana kowa na da hannu a ciki.
2: Ki Rika Shiga Mutane: Ki guji kadaita kanki saboda aurenki ya mutu. Shiga cikin mutane kiyi rayuwarki kamar yadda duk wata ‘ya mace take yi.
Yawan kadaita kai zai iya jawo miki fadawa wasu tunanin da zasu iya yiwa lafiyarki da rayuwarki illa.
3: Ki Kula Da Jikinki: Kada kice tunda aurenki ya mutu zaki daina kula da jikinki.
Yi kwalliyarki, gyara jikinki. Kashe dauri musamman idan zaki fita unguwa.
4: Samu Abun Yi: Idan daman kinada sha’awar karatu kuma kinada daman yi shiga makaranta.
Idan kasuwanci ko sana’a zakiyi dage kiyi. Kada ki sake ki zauna haka yadda zaki dogara da iyayenki ko zaurawanki.
5: Kada Ki Manta Da Abunda Ya Kashe Miki Aure: A kullum ya zama kina daukan abunda ya kashe miki aure da mahimmanci ba ki manta dashi ba ki sake yin kuskure.
Wani lokacin maza ne ke kirkiro matsalar da suke neman hanyar sakin mace. Wasu lokutan mugayen halayen mata ke jawo musu saki. Koma dai menene dalilin mutuwar aurenki, kada kiyi sakaci dashi domin kaucewa gaba.

Amincihausatv.com

6: Baiwa Wasu Mazan Dama: Wasu matan kuskure suke na kin kula wasu mazan da suke sonsu da aure bayan aurensu ya mutu.
Sam ba duk bane maza halayensu yake daya ba. Kada ki yiwa wani hukunci da laifin wani. Don haka baiwa wasu mazan dama cikin kiyayewa domin ganin yadda zasu taka nasu rawar.
7: Ki Danne Sha’awar Ki: Kuskuren da wasu mata zaurawa sukeyi shine na kasa danne sha’awar su na Jima’i bayan aurensu ya mutu.
Hakan yasa duk namijin daya zo da zancen aure ko soyayya sai kawai ki sakar masa gabanki. Daga bisa ki kasa samun mai son aurenki na gaskiya.
Tabbas macen data riga tasan dadin Jima’i hakurin rashinsa sai ta jimri, sai dai kuma wannan jimrin sune mutuncinta.
8: Ki Yarda Da Sulhu: Wasu lokutan bayan an rasa abunda ake da shi ne ake gane mahimmancinsa.
Kada ki ce bazaki baiwa tsohon mijinki dama ba idan yazama ya nemi kuyi sulhu.
Yana iya yiwuwa a wannan karon ya fahimci kuskurensa kuma zai gyara. Ci gaba da zama da gidan da kika saba idan akwai fahimta yafi zuwa sabon gidan da sabon rayuwa zaki soma dasu.
9: Kiyi Don Allah: Idan zaki koma gidanki ki koma saboda Allah da kuma zuciya daya. Hakan idan akwai dalilin da zai hanaki komawa ya zama hujjar da zaki bayar saboda Allah ba saboda son rai ba.
10: Kada A Miki Tarko Da Yaranki: Tabbas yara sunada matukar shiga rai, musamman wajen uwa. Sai dai kada hakan ne zai sa ki nace kina son komawa gidan mijinki.
Shi aure ba a zaman sa saboda yara, anayinsa ne saboda Allah domin ibada ne. Muddin ba zai a samu gyara a abunda ya jawo miki matsalar da mijin ba, idan kin koma saboda yara wahala da matsalar ba gyaruwa zasu yi. Su yara ko kina raye ko baki raye zasu rayu. Idan ubansu ko wata matarki gidan ta nemi cutar dasu damkasu hannnu wanda ya bakisu zai karesu. A matsayin ki na mutum kina son kema ki more rayuwar auren ki ne kamar yadda duk wata mace ke yi amma ba ki musgunawa kanki saboda yaranki ba.

Amincihausatv.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button