ylliX - Online Advertising Network Shekaru 7 Na Yi Ina Rubuta Waƙar Da Na Yi Wa Manzon Allah SAW Alan Waƙa - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Shekaru 7 Na Yi Ina Rubuta Waƙar Da Na Yi Wa Manzon Allah SAW Alan Waƙa

Shekaru 7 Na Yi Ina Rubuta Waƙar Da Na Yi Wa Manzon Allah SAW Alan Waƙa

Shahararren mawakin Hausar nan, Aminuddeen Ladan Abubakar wanda aka fi sani da Alan Waƙa ya ce ya dauki kimanin shekaru 7 ya na rubuta waƙar da ya yiwa fiyayyen halitta, Manzon Allah S.AW wacce ya sanyawa suna Muhammadu miftahul futuhati linzamin rayuwata

Yace ya kwashe shekarun ne kafin ya kammala rubuta waƙar saboda sai da ya gudanar da bincike mai zurfi, inda ya ƙara da cewa waƙar ta shafi tarihin rayuwar Annabi Muhammad (S A W) tun daga haihuwa har zuwa wafatin sa.

Irin wannan babban aiki yana matukar bukatar bincike na tarihi da kuma irin kalmomin da za’a yi su akan Fiyayyen Halitta, don gudun zarmewa Inji Alan waka

Hakazalika yace ita waka Mufitahul futuhati littafi ne ya mayar da shi waka saboda mutane da dama su amfana, inda ya ƙara da cewa babu shakka mutane sun ji dadin wakar kuma nima Ina alfahari da ita

Ya ce mafiyawan wakokinsa yana gina sune kan Ilimi kuma yana gudanar da bincike kafin yayi kowacce irin waka, inda ya ce domin yin hakan shi yake bani damar fadin abun da yake dai-dai akan duk wanda zai yiwa waka inji Aminu Alan Waƙa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button