LABARAI/NEWS

Shekaruna 2 ina kokarin shawo kanta har ta amince ta aureni, Mijin Bilkisu, Amaryar shekarun baya mai lalurar kafa

Shekaruna 2 ina kokarin shawo kanta har ta amince ta aureni, Mijin Bilkisu, Amaryar shekarun baya mai lalurar kafa

Shirin BBC Hausa na Mahangar Zamani ya samu damar tattaunawa da Bilkisu da mijinta Suleiman, inda suka bayyana kalubalen da suka fuskanta kafin aurensu ya tabbata.

Ta fara da bayyana cewa bata yi tunanin da gaske yake ba saboda akwai wadanda sukan je wurinta kamar da gaske daga baya kuma su shiririce.

A cewarta, a baya ta cire rai daga yin aure saboda lalurarta, amma sai ga shi Ubangiji ya azurtata da wanda ya ke son aurenta da gaske.

A bangarensa, kamar yadda ya shaida wa BBC Hausa, ya ce ya fara sonta ne bayan ta yi tsokaci a wani hotonsa, sai ya duba wasu wallafe-wallafenta a shafinta na kafar sada zumuntar zamani wanda take ba masu irin lalurarta kwarin guiwa.

A cewar mijin:

“Wallahi da na ga comment dinta a karkashin hoton da ni da mufti nayi, sai na bi fejinta sai na ganta. Daga nan dai kawai sai ta burge ni kai tsaye.

“Daya daga cikin dalilan shi ne, ba kasafai zaka ga mutum mai lalura ta musamman ba wanda zai tsaya wa kansa ba, har ma ya tsaya wa masu lalura irin tashi ba.

“Anan na ganta sai nace a’a gaskiya daga yau dai na zama masoyin abubuwa da kike yi da rubuce-rubuce da kike yi na kara wa mutane kwarin guiwa da kike yi. Kina burge ni, Allah ya taimaka.”
Ta fara da shaida yadda ta fara soyayya da wani likitanta wanda a lokacin da ta daina zuwa asibiti yake zuwa gida yana duba ta.
Kamar yadda ta ce:
“Shi likitana ne. A lokacin na daina zuwa asibiti, yana zuwa gida yana yi min. Sai a hankali ya fara nuna yana sona, don a lokacin aure ya fita a raina saboda gani nake yi ba zan taba aure ba.

“Kuma gani nake yi kamar wasa yake yi min saboda akwai wadanda zasu zo suce suna sonka, azo a dinga maka wasa da hankali daga baya su rabu da kai.

“To shi da ya nuna yana so sosai, sai nace to shikenan, ya gabatar da kan shi shima ya ce zai je gida ya yi musu magana.

“Da ya je gida ya yi magana, maman shi ta ce bata yarda ba. Ni kuma nace wallahi na hakura. Ya yi ya yi, nace a’a na hakura saboda ba zan iya aurenshi iyayenshi ba sa so ba.”

A lokacin da take soyayya da likitan, suna tare da Suleiman, mijinta na yanzu.

Kamar yadda mijin ya bayyana, sai da ya kwashe shekaru 2 yana kokarin shawo kanta, dakyar ta amince don da farko ta ce ta hakura da soyayya

Ya ce so da kauna ne suka sa ya jure ya kuma jajirce duk da wahalar da ya sha kafin ya samu ta amince ta aure shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button