Videos

Shin da gaske Abale likita ne kafin shigarsa kannywood ?

Dady hikima wanda kukafi sani da Abale anyi wani cece kuce akan sa wanda wasu ke ganin da yayi aikin likita kafin shigarsa hakar film yayinda wasu kuma ke ganin kawai shaci fadi wasu suke yi babu wata sana’ar da yayi kafin kannywood

A hakikanin gaskiya kafin shigar abale kannywood yakan zuwa asibiti domin aikin saka na neman lada wanda daman hakan ba saban abu bane ga wasu mutanen ana irin wannan aikin badan abiya kaba

Atun wata hira da BBC Hausa sukayi dashi inda yake fada musu cewa yayi karatun aikin lafiya wanda hakan harasa ya samu aiki ba shine yake zuwa asibiti domin ya taimaka sannan daga baya ya shigo harkar film

Ga masu bibiyar matashin jarumin sunsan yafi kwarewa akan acting din yan daba kona yan shaye shaye wanda hakan ne yasa wasu kin yadda kamar yadda jarumin ya fada abaya

Wasu suna daukar yadda mutum yake a film haka yake a zahirin gaskiya sai dai wannan ba fahimta bace me kyau yanzu dai gaskiya ta bayyana cewa Abale yayi aikin asibiti kafin shigowar sa kannywood

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button