ylliX - Online Advertising Network SHIN INTERFAITH ZAI YI MAGANIN TA'ADDANCI? - AMINCI HAUSA TV
FadakarwaLABARAI/NEWS

SHIN INTERFAITH ZAI YI MAGANIN TA’ADDANCI?

SHIN INTERFAITH ZAI YI MAGANIN TA’ADDANCI?

Manufar Interfaith a zahiri ita ce cire kiyayya tsakanin mabiya Addinai, don a yaki ta’addanci, a samu zaman lafiya tsakanin mutane.

Wannan shi ake bayyana wa mutane. Alhali Manufar Interfaith a bisa hakika ita ce cire kiyayya tsakanin mabiya Addinai, don a shafe rufin Addini a tsakaninsu.

Asali karfin kafircin Duniya (manyan kasashe) ne yake so ya shafe Addinai a bayan kasa, a koma rayuwar Ilhadi, ko alal akalli Gomnatocin kasashe su zama “Secular States”, wato kasashen da ba ruwansu da tsarin Mulki mai alaka da Addini ko dan kadan, wato Gomnatocin da ba ruwansu da Addini.

To tun tuni an gama da Addinin Kiris.tanci, babu abin da ya saura nasa sai dai a Coci. A Cocin ma idan ka leka Cocuna a Turai sai ka ga masu halarta ba su wuce ka kirga su a yatsun hanaye da kafafu ba.

Wannan ya sa sai aka ribaci ta’addancin da ake yi da sunan Addinin Muslunci, aka saukake masa hanyoyin yaduwa, don a nuna wa Duniya cewa; Muslunci Addinin ta’addanci ne.

Kuma idan an lura da kyau, wannan Ta’addanci da ake yi da sunan Muslunci ba kowa ya fi cutuwa da shi ba face Musulmai. Musulmai ake kashewa, su ake zuwa a samu a Masallaci suna Sallah a tayar da bama-bamai a kashe Masallata. Kafin a kai hari biyar wa Kiris.toci an kai hamsin wa Musulmai.

Don haka ba kin kafirai da Allah ya wajabta wa Musulmai ne ya kawo ta’addanci ba, balle a ce: za a kawar da ta’addanci ta hanyar Interfaith, a nemi zare wa Musulmai Akidar kin kafirai, a dasa musu Akidar soyayyar kafirai, alhali Allah ya hana hakan, inda ya ce:
{بَشِّرِ الْمُنَافِقِينَ بِأَنَّ لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا (138) الَّذِينَ يَتَّخِذُونَ الْكَافِرِينَ أَوْلِيَاءَ مِنْ دُونِ الْمُؤْمِنِينَ أَيَبْتَغُونَ عِنْدَهُمُ الْعِزَّةَ فَإِنَّ الْعِزَّةَ لِلَّهِ جَمِيعًا (139)} [النساء: 138، 139]

Ya ce:
{يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا الْكَافِرِينَ أَوْلِيَاءَ مِنْ دُونِ الْمُؤْمِنِينَ} [النساء: 144]

Ya ce:
{يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا الْيَهُودَ وَالنَّصَارَى أَوْلِيَاءَ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ وَمَنْ يَتَوَلَّهُمْ مِنْكُمْ فَإِنَّهُ مِنْهُمْ} [المائدة: 51]

Ya ce:
{يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا الَّذِينَ اتَّخَذُوا دِينَكُمْ هُزُوًا وَلَعِبًا مِنَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ مِنْ قَبْلِكُمْ وَالْكُفَّارَ أَوْلِيَاءَ وَاتَّقُوا اللَّهَ إِنْ كُنْتُمْ مُؤْمِنِينَ} [المائدة: 57]

Ya ce:
{تَرَى كَثِيرًا مِنْهُمْ يَتَوَلَّوْنَ الَّذِينَ كَفَرُوا لَبِئْسَ مَا قَدَّمَتْ لَهُمْ أَنْفُسُهُمْ أَنْ سَخِطَ اللَّهُ عَلَيْهِمْ وَفِي الْعَذَابِ هُمْ خَالِدُونَ (80) وَلَوْ كَانُوا يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالنَّبِيِّ وَمَا أُنْزِلَ إِلَيْهِ مَا اتَّخَذُوهُمْ أَوْلِيَاءَ وَلَكِنَّ كَثِيرًا مِنْهُمْ فَاسِقُونَ (81)} [المائدة: 80، 81]

Ya ce:
{يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا آبَاءَكُمْ وَإِخْوَانَكُمْ أَوْلِيَاءَ إِنِ اسْتَحَبُّوا الْكُفْرَ عَلَى الْإِيمَانِ وَمَنْ يَتَوَلَّهُمْ مِنْكُمْ فَأُولَئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ} [التوبة: 23]

Ya ce:
{يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا عَدُوِّي وَعَدُوَّكُمْ أَوْلِيَاءَ تُلْقُونَ إِلَيْهِمْ بِالْمَوَدَّةِ وَقَدْ كَفَرُوا بِمَا جَاءَكُمْ مِنَ الْحَقِّ} [الممتحنة: 1]

Ayoyi masu yawa, a cikinsu Allah yana hana rikan kafirai a matsayin masoya, majibinta, ko da kuwa iyaye ne, ko ‘yan’uwa na jini.

Miye ma’anar “Auliya’u”?

al-Ragib ya ce:
((الولاء والتوالي: أن يحصل شيئان فصاعدا حصولا ليس بينهما ما ليس منهما، ويستعار ذلك للقرب من حيث المكان، ومن حيث النسبة، ومن حيث الدين، ومن حيث الصداقة والنصرة والاعتقاد)).
المفردات في غريب القرآن (ص: 885)

((“Wala’i” da “Tawaaliy” shi ne a samu abubuwa guda biyu ko fiye, a same su ta yadda duk abin da ba su ba ba ya tsakaninsu. (Ma’ana; suna jere da juna, suna kusa da kusa babu komai a tsakaninsu). Shi ya sa ake amfani da kalmar ga kusaci na wuri, ko na dangantaka, ko na Addini, ko abota da taimakekeniya, da kusacin Akida)).

To ka ga a nan abin da ake yi na kokarin kusato da mabiya Addinai kusa da juna, a cire kiyayya a tsakaninsu, a mai da su su zama abokan juna masoya, a kusato da fahimtar Addinan kusa da juna, a nuna ai kusan abu daya suke, wannan abu ne da Allah ya hana a cikin wadancan Nassoshi da suka gabata. Wannan kuwa shi ne aikin Interfaith, da kowane irin ma’ana aka fassara shi.

Saboda haka tambaya ta gaba ita ce; me ya kawo ta’addanci?

Abin da ya kawo ta’addanci abubuwa ne masu yawa, amma za a iya dunkule su cikin abubuwa guda biyu:

1- Yakar Muslunci da manyan kasashe suke yi:
Yadda karfin kafircin Duniya ta hanyar manya kasashe yake amfani da karfi ta kowace fiska yake yakar Addinin Muslunci, da hana samar da Gomnatoci masu gudanar da Shari’ar Muslunci shi ne babban sababin da ya haifar da ta’addanci.

2- Jahiltar Addini daga Khawarijawa:
Su wadannan Khawarijawa ‘Yan Ta’adda, wadanda suke kafirta Musulmai, su halasta jinanensu, suna yin haka ne saboda sun jahilci hakikanin Addini, suna daukan sashen Nassoshin Shari’a suna barin wasu sashen, kuma suna dora Nassoshin da suka sauka a kan kafirai, suna dora su a kan Musulmai, sai suke kafirta Musulmai, musamman saboda gurguwarr fahimta da suka yi mas’alar “Hukunci da abin da Allah ya saukar”, wacce ake kira da “Hakimiyya” a wannan zamani. Wannar shubuha ita ce ainihin shubuhar Khawarijawan farko, har zuwa wannan zamani.

Wadannan su ne manyan sabuban faruwar ta’addanci, kuma su ne muhimmai. Don haka idan ana so a yi magananin ta’addanci, dole sai an magance wadannan matsaloli guda biyu.

Dole sai manyan kasashen Duniya, masu neman shafe Addinai a bayan kasa, musamman Addinin Muslunci, sai sun bar Musulmai sun yi Addininsu, sun kafa Gomnatoci a kasashensu, masu bin tsarin Shari’ar Muslunci, in ba haka ba kuma Ta’addanci ba zai kare ba.

Haka kuma dole sai an yaki jahilcin da ke cikin al’ummar Musulmai, musamman wadanda suka yi masa gurguwar fahimta, sai an yi bincike an gano mabullar wannan jahilci, wanda aka kunshe a cikin “HAKIMIYYA”, ake kafirta Musulmai, ake halasta jinanensu.

Kuma abin da manazarta suka tabbatar shi ne a wannan zamani, wannar Akida ta Khawarijanci ta bayyana ne ta hanun Sayyid Qutub, bayan ya dauko daga al-Maududiy. Shi ya sa kusan za ka iya cewa; ba a taba ganin kafirta Musulmai irin wanda aka gani a wajen Sayyid Qutub ba, inda ya nuna cewa; tun karnonin baya masu yawa mutane suka yi ridda suka koma Jahiliyya.

Kai, a wannan kam, hatta Khalifancin Sayyidina Usman (ra), da kuma na Mu’awiya (ra) da khalifofi a bayansa, in ka cire Umar bn Abdil’azeez (ra) ba su tsira a wajen al-Maududiy ba, ya ce: sun koma Jahiliyya, duka bisa da’awar an bar “HAKIMIYYA’.

Saboda haka magana ta gaskiya, tsarin Interfaith da Gomnatoci suka dauko da sunan yakar ta’addanci a bisa hakika ba maganin Ta’addanci ba ne, asali ba don yakar ta’addancin aka kirkire shi ba, an kirkire shi ne don ya dasashe haske da karsashin Addinai. Don su kuma gomnatoci su samu daman hada kan mutane, don su ji dadin mulkansu cikin sauki, nesa da maganar Addini.

Dan haka idan ta’addanci ake so a yaka da gaske, to dole sai manyan kasashe sun bar Musulmai su yi Addininsu, su kafa Gomnatoci na Shari’ar Muslunci akasashensu.

Sai kuma Malamai su tashi tsaye su yaki Fikrorin Khawarijanci da suka shigo cikin al’umma ta hanyar al-Maududiy da Sayyid Qutub, a koya musu Akida ingantacciya, a yaye musu shubuhohinsu, a seta kwakawlensu da tunaninsu, su dena kafirta al’umma suna halasta jinanensu.

Amma fa ko na biyun ya ci nasara, idan manyan kasashe da karfin kafircin Duniya bai dena yakar Muslunci ba, tsugune ba ta kare ba, kuma su manyan kasashen ba za su dena ba.

Don haka a takaice, kawai a dena yaudarar mutane da Interfaith da sunan neman zaman lafiya, ana zagwanye wa Musulmai Akidar kiyayyar kafirai, alhali Allah ne ya umurce su da ita.

Dr. Aliyu Muh’d Sani

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button