LABARAI/NEWS

Shin kunsan ‘yar wasan guje guje da ta zama mataimakiyar, kwamishinan yan sandan Najeriya

Shin kunsan ‘yar wasan guje guje da ta zama mataimakiyar, kwamishinan yan sandan Najeriya

‘Yar Najeriya Chioma Ajunwa ita ce mace ta farko kuma daya tilo da ta shiga gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA a matsayin ‘yar wasan kwallon kafa da wasannin Olympics a matsayin ‘yar wasan guje-guje da tsalle-tsalle.

Ta kasance a gasar cin kofin duniya ta mata na FIFA karo na farko a kasar Sin a shekarar 1991. Tana taka leda a matsayin mai kai hari.

A gasar Olympics ta lokacin rani da aka yi a Atlanta a shekarar 1996, ta ci lambar zinare a tsalle mai tsayi, kuma har ya zuwa yanzu ta kasance daya tilo da ta samu lambar zinare a Najeriya.

Ita ce Bakar fata ta farko da ta samu lambar zinare a gasar Olympics a fage a halin yanzu ta shiga aikin yar sanda, ta kuma samu matsayin mataimakiyar kwamishinan yan sanda wata majiya ta ce yanzu tana matsayin kwamishiniyar yan sanda.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button