LABARAI/NEWS

Shugaba Buhari Bai Gaza Ba, Munanan Halayenmu Ne Su Jefa Nijeriya Cikin Kunci?

Shugaba Buhari Bai Gaza Ba, Munanan Halayenmu Ne Su Jefa Nijeriya Cikin Kunci?

Kuyi Zina
Kuyi Luwadi
Kuyi Madigo
Kuyi fyade
Kuyi istimna’i
Kuyi chacha
Kuyi sata
Kuyi tsafi
Kuyi bokanci
Kuyi shirka
Kuyi karya
Kuyi yaudara
Kuyi cin amana
Kuyi ha’inci
Kuyi zamba cikin aminci
Kuyi algus
Ku kalli blue fim
Ku kalli hotunan batsa
Ku zagi Malamanku
Ku zagi shugabanninku
Ku zagi Sarakunanku
Ku zagi jami’an tsaronku
Ku wulakanta Al-Qur’ani
Ku jefa Qur’ani cikin toilet
Ku zagi Sahabban Annabi (SAW)
Ku zagi matayen Annabi (SAW)
Ku zagi iyayen Annabi (SAW)
Ku zagi Annabi (SAW)
Ku tauye mudu
Satar waya a unguwa
Satar takalmi a masallaci
Satar mashin a Makabarta
Satar makirfon a Masallaci

Amma daga anyi magana sai kaji kun fara babatu wai shugaba Buhari ya gaza, kuna aikata irin wannan muggan laifuka da sabon Allah kuma kuyi tunanin Allah Ya kyaleku haka?

Na fada na kara fada Shugaba Buhari bai gaza ba, laifukanmu ne Allah Ya ke nuna mana izna a kansu ko zamu gyara, amma muddin muka tafi a haka ko shekara nawa zamuyi zamu dawwama ne a cikin wannan yanayi

Ya Ubangiji Allah Ka dube mu da idon Rahama ba don halinmu ba, Ka kawo mana dauki da mafita na alheri.

Daga Elmu’az Lere

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button