LABARAI/NEWS

Shugaba Buhari ne ya ce kada mu saka sunan Osinbajo a kwamitin yaƙin zaɓen Tinibu

Shugaba Buhari ne ya ce kada mu saka sunan Osinbajo a kwamitin yaƙin zaɓen Tinibu

Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Jam’iyyar APC mai mulki ya yi ƙarin haske kan dalilin da ya sa ba a saka sunan mataimakin shugaban ƙasar Farfesa Yemi Osinbajo ba cikin kwamitin yaƙin neman zaɓe na Asiwaju Bola Tinubu.

A yau ne dai aka fitar da sunayen mutum 422 waɗanda za su jagoranci yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar APC

Ƙaramin Ministan Ƙwadago na Najeriya Festus Keyamo wanda shi ne kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen ya tabbatar da cewa Shugaba Buhari ne ya ce kada a saka sunan Osinbajo da sakataren gwamnati Boss Mustapha saboda za su mayar da hankali ne kan gudanar da ayyukan gwamnati.

Keyamo ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar sakamakon ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan sunayen da aka fitar Ya ce Buhari a matsayinsa na shugaban kwamitin, shi ya bada umarnin kada a saka Osinbajo da Mustapha.

Ya ce dama gwamnati da ta damu da talakawa ba za ta bari duk jami’an gwamnati su bar ayyukansu su tafi harkar siyasa ba Osinbajo dai na daga cikin waɗanda suka nemi tsayawa takarar shugabancin Najeriya a APC sai dai bai samu nasara ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button