ylliX - Online Advertising Network shugaban Amurka ya yi wa duk yan wiwi afuwa - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

shugaban Amurka ya yi wa duk yan wiwi afuwa

Shugaban Amurka Ya Yi Wa Duk Ƴan Wiwi Afuwa

Joe Biden na Amurka ya fitar da wani umarnin shugaban ƙasa inda ya yi afuwa ga duk Amurkawan da kotunan tarayya suka samu da laifi saboda kawai an kama su da tabar wiwi

Rahotanni sun ce matakin zai shafi akasari mutane ƙalilan ne na hukuncin da ke da alaƙa da tabar wiwi saboda mafi yawa a kotunan jihohi ake ƙarar su

Kaɗan ya rage sanarwar Shugaba Biden ta halasta tu’ammali da wiwi, kamar yadda ya yi alƙawari lokacin da yake yaƙin neman zaɓe

Ƙuri’un jin ra’ayoyi na baya-bayan nan sun nuna cewa mafi yawan Amurkawa sun yi imani cewa kamata ya yi a halasta sha da dillancin tabar wiwi

Aika mutane zuwa gidan yari saboda suna ɗauke da wiwi ya birkita rayuwar mutane fiye da adadi kuma a tsare mutane saboda halayyar da jihohi da dama a yanzu ba sa hanawa in ji sanarwar Joe Biden ta ranar Alhamis.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button