LABARAI/NEWS

Shugaban kasa Buhari ya karrama ɗan Daudu kuma mai fafutukar halatta Auren Jinsi a Nigeria

Shugaban kasa Buhari ya karrama ɗan Daudu kuma mai fafutukar halatta Auren Jinsi a Nigeria

A Ranar Talata 11 ga watan Oktobar 2022 ne shugaban Najeiya Muhammadu Buhari ya jagoranci bikin karrama ƴan ƙasa waɗanda suka bawa al’umma gudummawa a matakai daban-daban na rayuwa, Sai dai taron ya bar baya da kura.

Kazalika, Ƴan Najeriya da dama a kafofin sadarwa zamani suna ta tofa albarkacin bakin su yayin da aka hango wani fitaccen ɗan ƙungiyar ƴan Luwadi Mr. EZRA OLUBI a cikin waɗanda aka karrama da lambar yabon ta OON (Order Of The Niger)

AMMA MUYI ADALCI Ga duk wanda ya kalli bidiyon an gano shi kansa Buhari ya saki baki yana kallon yanayin shigar Olubi wanda ciki harda bakin jan-baki ya goga a labban sa da wannan shigar kayan da ya yi.

Babban abun tambayar shi ne shugaban ƙasa ne yake zaɓo mutane? Ko kuma wasu ne suke zaɓo fitattun mutanan domin a karrama su idan haka ne menene ribar su na zaɓo irin su Ezra ko dai suna da alaƙa ne?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button