Fadakarwa

SIRRI GAME DA NONON MACE

A RIƘA YI ANA LURA DA JIKI
📚📚📚📚📚📚📚📚📚📚📚📚📚

Breast ɗaya yaɗan ɗara daya girma wannan “is perfectly normal” Babu wani abun damuwa ganin hakan ƴan Mata. Haka ma ko Maza galibi jakar ƴaƴan maraina guda kan ɗara guda girma duk normal ne muddin ba ciwo ko wani abu ake ji ciki ba.

Shi Nono gaba ɗaya jin wani abu ciki kamar ƙullutu a guda ɗaya ko duk biyun ako yaushe shine abun ai binkice, har sai in bayan an tabbatar bawani abu bane mai hatsari tukun.

Saboda akwai toshewar bututun nono da yana sa aji lump ga wacce ke Shayarwa, ko kuma sansomin wani canji da in ba ai wani abu ba ka iya zama cancer musamman in babu wani tarihin taɓa bigewa a nonon, tun da sankarar nono nada cuttukan cancer 5 dake muna kisa yanzu a Nigeria. In duk Matan da kika sani zasu ce suna da kullutu a nono hakan bai nuna duk normal.

Breast cancer itace ma kan gaba. Da yawa na mutuwa ba’asan me ya kashe su ba tun da mutanen mu ko basu lafiya sai sun ji ba sarki sai Allah sun gama galabaita sannan sukan nufi asibiti. Don haka EARLY DETECTION ALWAYS SAVES LIVE. Ana son akalla duk shekara aje screening inda hali.

RED FLAG 🚩

◽Jin ƙullutu,
◽Ganin ruwa me jini-jini na fita daga nono,
◽Ganin jikin nono ya ɗan lotsa kamar dimples,
◽Ganin fatar nono ta canza zuwa jajur tana zafi in antaɓa,
◽Ko fatar nono ta canza kamar jikin lemon ɓawo

Wadannan abubuwan 5 basa taɓa zamowa normal a nono har sai anje ga likita ya bincika ya tabbatar da komi lafiya, inko baki gamsu ba toh duk da haka kya kuma zuwa kiji ra’ayin wani likitan. Ki nutsu a binkiceki da kyau.

Kusani idon da kike tunanin dashi likita ke kallon ki ba haka abun yake ba. Likita baya yankewa mutane hukunci, rantsuwa yai zai kare lafiya, duk wani abu da zaki faɗa sama da sau ɗari yaji wanda ya fisa.

Bazai taɓaki ba saida izini sai kuma da wani naki tsaye saide inkinqi, ko kinqi Mace yar uwar ki ta tsaya toh bazai rufe kofa ba ka’ida kenan… Ki tsaya adubaki in kuma Mace ce likitar Toh ta duba ki yafi ai magana da baki Ace ana tunanin ba Matsala, duban da likita zai miki (inspection, palpation) yafi amfani 80% cikin 100 fiye da Turaki scanning da ka, duk da can ma tubewa zaki.

Don haka ba ruwan likita da matsalar ki a nono take ko farji, yaga nonuwa sunfi karfin kirgawa, har yankawa da hannun mu munyi sau ba adadi, walau a mutum me rai ko gawa. Kurum ki nutsu ki bamu amsar kowacce irin tambaya da za’a jeho miki.

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

Haka nan kaima Goga don ka auro budurwa kar kaji ance tsayayyen nono ka ɗauka baza kaga sun rusuna ba, Ba irin waɗancan nonuwan da ka saba gani a pornographic contents bane, suma waɗancan breast augmentation ne kudi suka kashe aka sa musu silicone aka tsaida amma ba natural bane, dole breast ya sunkuyo malam.

Don haka kar kaje kana zarge-zargen banza, ana iya samun nonon mai shayarwa da yafi na budurwa a tsaye hakan bai nuna wannan budurwa ta rika aikata wani abu…

Sama da sau 50 ma kila tafi ka, kila duk ka tatsile kanka wajen masturbation ma amma wai kai ka baza ido kaga abu tsaitsaye. A dena ruduwa da da finafinan batsa gaskiya a ciki 20% ce kurum sauran 80% duk karya ne “Is FAKE”.

A KARSHE

Kowa ya lura da tsaftar jiki, matse-matsi, hammata da wanke jiki baki daya sau biyu a yini, arika motsa jiki, arika sa kaya masu tsafta in a sami hali ake fesa turare… hakan na qara lafiya da nutsuwa koda aljihu babu kudi.

✍🏻
[Ibrahim Y. Yusuf]

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button