LABARAI/NEWS

Sojin Najeriya sun kashe manyan kwamandojin Boko Haram Hedikwatar tsaron Najeriya

Sojin Najeriya sun kashe manyan kwamandojin Boko Haram Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun kashe manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram a cikin mako biyu da suka gabata

A wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis rundunar tsaron ta ce dakarun Operation Hadin Kai ne suka kashe kwamandojin ta hanyar yi musu ruwan bama-bamai a maɓoyarsu

Hedikwatar tsaron ta ce dakarun sun kuma halaka sama da ‘yan ta’adda 57 a wurare daban-daban bayan samame da suka kai tsakanin ranakun 11 zuwa 25 ga watan Agusta a yankin arewa maso gabashin kasar

 

 

 

Shugaban sashen harkokin yaɗa labarai na rundunar Manjo Janar Musa Danmadami ya bayyana cewa samamen sun kunshi wanda aka yi ta sama da kasa a kan maboyar mayakan na Boko Haram da na ISWAP a jihohin Borno da Yobe

 

Danmadami ya ce daya daga cikin kwamandojin da aka kashe shi ne Uzaifa, wanda yake cikin manyan jagororin kungiyar hudu
Ya kara da cewa an kama mutum takwas da ake zargi na aikata ta’addanci da kuma hudu da ke kai wa ‘yan bindiga makamai, inda aka ceto fararen hula hudu

 

A cewarsa yan Boko Haram aƙalla 1,652 da iyalansu ne suka mika wuya ga dakarun Najeriya a wurare daban-daban a baya-baya nan Daga cikinsu akwai maza 320 da mata 442 sai kuma yara 890

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button