ylliX - Online Advertising Network Sojin Sama Sun Hallaka Shugaban Ƴan Bindiga Ali Dogo Da Wasu 30 A Kaduna - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Sojin Sama Sun Hallaka Shugaban Ƴan Bindiga Ali Dogo Da Wasu 30 A Kaduna

Sojin Sama Sun Hallaka Shugaban Ƴan Bindiga Ali Dogo Da Wasu 30 A Kaduna

Sojojin Najeriya sun kashe wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga a jihar Kaduna, Ali Dogo, da mayakansa 30, kamar yadda PRNigeria ta rawaito.

An bayyana cewa, an kashe Dogo, wanda aka fi sani da Yellow, tare da ‘yan kungiyarsa, sakamakon harin da jiragen yakin rundunar sojin sama su ka kai a karshen mako.

Da ta ke tabbatar da tashin bama-baman kan Yellow da mayakansa, wata majiyar leken asiri ta tsaro ta shaida wa PRNigeria cewa fitaccen shugaban ‘yan bindigar, da ‘yan ta’addansa sun gudu daga jihar Neja zuwa wani gidan Alhaji Gwarzo da ke Yadi a Ƙaramar Hukumar Giwa domin tsira da rayukansu, sakamakon ci gaba da ruwan bama-bamai da jiragen NAF suka yi akan maɓoyarsa a Neja a kwanan nan.

Majiyar ta ce Abin takaici ga Yellow da mayakansa, yayin da su ke cikin taro, jirgin NAF ya kai hari gidan Alhaji Gwarzo, wanda ya sa duk wanda ke cikin ginin ya hallaka su ciki har da Yellow din

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button