LABARAI/NEWS

Sojoji sun kwace gari na karshe daga hannun Boko Haram a Borno

Sojoji sun kwace gari na karshe daga hannun Boko Haram a Borno
Rundunar sojin Najeriya ta kwace gari na karshe wato Guduumbale da ke jihar Borno

a arewa maso gabashin kasar daga hannun mayakan Boko Haram
Bisa bayanan da sashen Hausa na RFI ya tattara, ya gano cewa har yanzu wannan gari babu kowa a cikinsa face sojoji, sai kuma daidaikun Fulani da dabbobinsu

Musa Ibrahim da ya bi ayarin gwamnatin jihar Borno zuwa wannan gari, ya yi mana karin bayan kan abin da idansa ya gane masa

Akalla mutane dubu 40 ne suka rasa rayukansu a yankin arewa maso gabashin Najeriya, yayin da kimanin miliyan biyu suka tsere daga muhallansu tun daga shekarar 2009 sakamakon hare-haren mayakan Boko Haram

Rikicin na Boko Haram ya yadu zuwa kasashe makwabta da suka hada da Chadi da Kamaru da Nijar, lamarin da ya jefa al’ummar yankin Tafkin Chadi cikin garari

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button