Sojojin Nigeriya Sun Kai Mummunan Hari A Gidan Bello Turji Sun Kashe Yan Bindiga 12

Sojin sama sun kai samamen sa duka kai gidan Bello Turji sun kashe yan bindigarsa 12 a Zamfara hakan tasa shi ogan ba farce da gudu yayi cikin daji
Akalla yan bindiga 12 ne sojin saman Nigeriya suka halaka har lahira a wane samame ta sama da suka kai gidan dan bindiga Bello Turji a ana tsaka da bikin radin suna
cewa sai dai lokacin da sojin suka kai harin Bello Turjin ba shi a gidan sai dai wasu hadiman sa da yake ji da su da kuma sauran yaran sa amma bayan haka shima an bishi amma bai kamu ba
Lamarin ya afku a ranar Asabar a lokacin da yan bindigar ke tsaka da gudanar da bikin sunan dan Bello Turji a kauyen Fakai dage cikin yankin karamar hukumar Shinkafin jihar Zamfara
Shedun gani da ido sun tabbatar wa majiyar tamu da faruwar lamarin sai dai da suka tuntubi Kakakin sojin saman dake kula da shiyar Katsina da Zamfara bai amsa kiran waya ba domin ji ta bakin sa