ylliX - Online Advertising Network Sojojin ruwa sun kuɓutar da ƴan mata 50 s gidajen karuwai a Port Harcourt - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Sojojin ruwa sun kuɓutar da ƴan mata 50 s gidajen karuwai a Port Harcourt

Sojojin ruwa sun kuɓutar da ƴan mata 50 s gidajen karuwai a Port Harcourt

Rundunar sojin ruwan ta ƙasa ta ce ta ceto karuwai 50 tare da cafke wasu mutane uku da ake zargi da kawalcin ƴan mata a wani samame da su ka kai a wasu gidajen karuwai biyu na Port Harcourt.

Richard Iginla, Jami’in yada labarai na rundunar ne ya yi holon wadanda ake zargin tare da waɗanda a ka ceto a gaban manema labarai a Port Harcourt a yai Lahadi.

Iginla, mai muƙamin Laftanar-kwamanda ya ce an gudanar da aikin ne tare da hadin gwiwar hukumar hana fataucin bil’adama ta ƙasa, NAPTIP da kuma jami’an tsaron farin kaya na Najeriya, NSCDC.

A cewarsa, karuwai 50, galibi ƴan mata matasa ne aka ceto da sanyin safiyar Asabar bayan da hukumar NAPTIP ta basu bayanan sirri.

Mun samu bayanan sirri ne daga hukumar ta NAPTIP, wacce ta rika bin gidajen karuwai da su ke tara ƙananan yara, inda wasu ma daga cikinsu ‘yan kasa da shekara 14 ne.

Don haka, bayan da hukumar NAPTIP ta sanar da mu, sai a ka kafa wata tawaga ta hadin gwiwa, nan take muka shiga aikin ceto wadanda lamarin ya shafa.

An ceto ƴan mata sama da 50 da aka tilastawa yin karuwanci yayin da aka kama masu daukar su zuwa karuwanci su uku in ji shi.

Iginla ya ce an rufe gidajen karuwai da su ka haɗa da Royal Brothel da Cool Breeze Brothel da ke kan titin Azikiwe a unguwar Diobu a Fatakwal.

Ya ce ana ci gaba da bin diddigi tare da kame shugabannin kungiyar masu kawalci, wadanda ke daukar yara daga kauyuka zuwa karuwanci

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button