LABARAI/NEWS

Sojojin sama sun dagargaza dabar ƙasurgumin ɗan fashin dajin da ya addabi Zamfara da Katsina

Sojojin sama sun dagargaza dabar ƙasurgumin ɗan fashin dajin da ya addabi Zamfara da Katsina

Rundunar sojin saman Nijeriya ta tabbatar da nasarar dagargaza dabar ƙasurgumin ɗan bindiga kuma mai garkuwa da mutane da ya addabi jihohin Zamfara da Katsina wato Halilu Tubali.

Kamar yadda rundunar ta tabbatar wa BBC Hausa, sun kai ma sansanin ɗan bindigar hari ne a ranar Juma’a bayan sun sami bayanan sirri suna gudanar da taro a gidan nasa.

Kamar dai yadda Katsina Daily News ta ruwaito, “duk da wasu sun bayyana cewa Halilu Tubali yana cikin waɗanda aka kashe, amma rundunar ta tabbatar da cewa babu wani abun da za su kara mora a cikin gidan nasa, saboda sun dagargaza shi

Wanne fata ko kalaman kwarin gwiea za ku yi wa jami’an tsaron Nijeriya kan kokarin da suke yi wajen dakile ta’addanci a kasar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button