ylliX - Online Advertising Network sojojin sama sun kashe fitaccen dan bindiga da matan sa biyu da kwamandojinsa 8 - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

sojojin sama sun kashe fitaccen dan bindiga da matan sa biyu da kwamandojinsa 8

Yadda rundunar sojin sama suka kashe fitaccen dan bindiga matan sa biyu da kwamandojinsa 8 a Katsina Yadda sojojin sama sun ragargaza sansanonin ‘yan bindiga a jihohin Katsina Zamfara Sokoto da Kaduna

A wani luguden bamabamai da sojojin saman Najeriya suka yi a cikin makon jiya sun samu nasarar gamawa da wani fitattcen dan bindiga da ya buwayi mutane a jihar Zamfara mai suna Abdulkarimu da aka fi sanin sa da Faca-Faca, matan sa biyu da manyan kwamandojinsa

Rundunar ta kai wa Faca-Faca hari a kauyen Marina dake karamar hukumar Safana jihar Katsina
jami’an tsaron sun kai wa Faca-Faca hari bayan samun bayanan siri game da inda yake kwana

kakakin rundunar Ƴansandan Jihar Katsina SP Gambo Isa ya tabbatar da harin inda ya ce Rundunar sojin sama sun kashe mutum takwas da ake zargi ‘yan bindiga ne da shugaban su Faca-Faca Wasu daga cikin maharan sun gudu

Dan majalisar dokokin jihar AbdulJalal Runka ya tabbatar da aukuwar wannan aiki da sojoji suka yi Sannan wasu mazaunan Safana su biyu sun bayyan wa cewa mutane da dama sun gudu sun bar gidajen su a dalilin wannan farmaki kan yan bindiga da sojoji suka kaiFaca-Faca

Wani mazaunin Safana Shamsu Masud ya ce Faca-Faca ya dade yana kawo wa kauyukan dake karkashin kananan hukumomin Safana, Danmusa, Batsari da wasu bangarorin jihar Zamfara hari
Shidai Faca faca ana zargin yana cikin Ɓarayin da suka Jagoranci kitsa harin da aka kaiwa Motocin Jami’an tsaron fadar Shugaban ƙasa akan hanyar su ta zuwa Katsina ƙwanakin baya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button