Subhanallah Mr 442 da safara’u suna Bata Tarbiyyan yara matasa Dole hukuma ta dauki mataki

Subhanallah Mr 442 da safara’u suna Bata Tarbiyyan yara matasa Dole hukuma ta dauki mataki
Wannan ba karamar masifa bace wa’yannan mawakan suka zo ta iya ku duba kuga yadda kananun yara suke koyi dasu wajen yin waka da kuma rawa wanda hakan ba karamin abin kunya bane a wajen musulmi baki daya ace kana da yarinya yar karama amma tana koyi da wa’yannan mawakan
Idan kuka kalli cikin wannan bidiyin zakuga yadda wata yar karamar yarinya take tika rawa akan wata wakar safara ‘u abun babu dadin kallo ga duk wanda ya kalli wannan bidiyon sai kunya ta lullube shi
Yarinyar da batafi shekara biyar ba amma ta iya ta Koyi rawa ta mararsa tarbiya wanda kuma annsan wa’yanda suka fara hassasa wannan rawar lallai Yakamata a fara daukar mataki akan wannan abubuwan domin ba’a san nangaba masifar da zasu janyoba
Mutane gari sunyi kyakkyawan kira ga hukuma domin ta dauki mataki domin a hankali wa’yannan mutanen suna bata tarbiyyar kananun yara harma da manya suna koyi da wa’yannan mawakan
Abin kunyar ma shine idan mutum ya kunna wayar hannunsa zaiyi wuya baiga wata sabuwar fitsarar na wacce suka kara fito da ita mudai Allah ya shirya mana zuri’a