Videos

Ta Tabbata Ado gwanja zai Angonce Da jaruma momee Gombe akwai shagalin bikin a kannywood

Ta Tabbata Ado gwanja zai Angonce Da jaruma momee Gombe akwai shagalin bikin a kannywood

Yanzu dai ta tabbata wannan mawakin zai angonce da daya daga cikin manyan jarumai wacce a yanzu tana daga cikin wanda tauraruwarsu take haskawa kuma take cikin wa’yanda suka iya rawa dama dukkan Wani abu da ake son jarumi ko jaruma su kasance duka wannan jarumar ta haɗa

Sai gashi inda take a matsayin allura cikin ruwa sai mai rabo ashe rabon mawaki Ado gwamja ce yanzu shine wanda zai kasance mujinta kuma uban ƴaƴanta idan Allah ya yarda inda suka sasanta kansu kuma ciniki yana nema ya fada

Yanzu lokaci kawai ake jira domin duk wani shirye shirye yayi nisa a wannan masana’anta na wannan bikin saboda bikine wanda zai yi matukar dadi da kuma jan hankali saboda wannan mawakin babu mawakin mai yawan masoya mata kamar sa

Sai dai wani abu da mutane basu saniba shine wannan jarumar fa kowa yasan ta taba yin aure a baya sai dai har suka rabu da wannan mijin nata bata samu ta haihuwa shine ake kiranta da sakin wawa wanda ashe rabon ado gwanja ce zai kara samun ta a matsayin mata kuma gashi daman dukkansu yan masana’anta daya ne kusan kowa yasan halin kowa

Acikin hotunan da suka saki sunyi matukar dacewa da juna saboda wasu ma cewa suke wannan jaruma daman chan ado gwanja ne ya dace da ita ba wani ba

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button