TA’ADDANCI KUNGIYAR OPC A KAN YAN AREWA BISA KIN TSAWATARWAR BOLA TINUBU. KASHI NA FARKO.

TA’ADDANCI KUNGIYAR OPC A KAN YAN AREWA BISA KIN TSAWATARWAR BOLA TINUBU. KASHI NA FARKO.
OPC dai ita ce ke da alhakin tashe-tashen hankula da dama kuma mambobinta sun kashe ko jikkata daruruwan mutane. Yayin da mafi yawan munanan hare-haren da suka kai kan Hausawa ne, ko kuma mutanen da ake zargin ’yan Arewa ne, wadanda abin ya shafa sun hada da Ibo da Ijaw da kuma mutanen wasu kabilun, Da yan sanda.
Shedun gani da ido da dama da kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta tattara sun tabbatar da cewa sabanin yadda shugabanninsu suka musanta, kungiyar ta OPC ta yi amfani da makamai iri-iri da suka hada da bindigogi, Adduna, wukake. Haka kuma Sun zuba acid a jikin wadanda abin ya shafa. Sau tari sukan cinnawa gawarwakin wadanda suka kashe wuta, wani lokaci bayan sun yanka su. Yana da wuya a iya tabbatar da inda OPC Su ka Samo makaman da Su ka yi amfani da su. Kananan makamai na yaduwa a Najeriya kuma yana da saukin sayen bindigogi da sauran makamai. Kazalika, wasu lokutan OPC na kwace wasu makamai na ‘yan sanda ko kuma wadanda ake zargi da aikata laifuka da ta kama a lokacin da suke aikin banga.
Rikicin Kabilanci
An dai sha samun irin kashe-kashe da OPC ta yi a cikin rigingimu ko rikici da wasu kabilu tun a kalla a shekarar 1999. A lokacin Mulkin Tinubu, Sau da yawa wadannan fadace-fadacen sun samo asali ne sakamakon wata ‘yar gardama tsakanin wasu mutane biyu da suka fito daga kabilu daban-daban, wanda A lokacin yawanci Fada sai ya barke. Jam’iyyar Yarbawa ta shigo da OPC domin yaki Saboda Kare manufarsu, yayin da sauran kabilan suka mayar da martani inda suka kira matasan al’ummarsu da su kai dauki. Lamarin yakan rikide da sauri zuwa wani rikici na kabilanci cikin sa’o’i, ko kuma a wani lokaci cikin mintuna.
Za’a Ci Gaba.