Latest Hausa Novels

TABBAS ALLAH YA ISA

TABBAS ALLAH YA ISA…

Safiyar jiya LAHADI Misalin karfe goma na safe wani mai mota yayi fatali da kayan tallan raken wani MATASHIN DATTIJO, maimakon mai motar ya bashi hakuri sai yaci magani yaƙi yace komai, duk ya zube a kwata, mai raken yazo gaban mai motar yace ME YASA KA ZUBAR MIN DA RAKE? MAI MOTAR ya kalleshi yace uban wa yace ka tare hanya?

Mai rake yace babu inda na tare hanya kai dai kawai ka zalinceni, kawai ka biyani, nan da nan mai motar ya hau shi da zagi yana cewa anƙi a biya ɗin, cikin hawaye mai raken yace bakasan wahalar da nasha na sami jarin ba, amman ka zubarmin ka cuceni ka cutar da rayuwata.

MAI MOTAR ya ci gaba da zaginsa, MAI RAKE ya kalleshi yace DA ƘARFIN IKON ALLAH SAI UBANGIJI YA GAGGAUTA YIMIN SAKAYYA, ALLAH YA ISA!! ALLAH YA ISA!! ALLAH YA ISA!!! Sau uku yana faɗe, babu yadda banyi ba akan mai MOTAR ya daina zaginsa sannan ya biya shi haƙƙinsa, amman sai ya haɗa har da ni yana zagi, munaji muna gani mai motar yayi gaba abinsa bai biya shi komai ba ya tafi.

MAI RAKE YACI GABA DA ZUBDA HAWAYE, tausayinsa ya kamani sai na zaro kuɗi na biya kuɗin raken duka sannan na ƙara masa da wani abu, Wallahi sai naga yana kukan farin ciki a karo na biyu, yanata yi min addu’a, tare da cewar Ubangiji ya ninka maka fiye da abinda ka tallafamin, nayi gaba na barshi yana ta addu’a.

Banfi minti uku ba daidai Tal’udu Juction naci karo da wata tsohuwar ƙawata da mukayi FCE KANO da ita, munfi minti goma muna hirar yaushe gamo, da zamu rabu tace bari in baka kuɗin mai, wallahi sai da ta ninkamin abinda na baiwa mai raken nan sau 16 tare da wasu canji, take sai addu’ar mai rake ta faɗo min da yace Ubangiji ya ninka maka fiye da abinda ka bani, azuciyata nace TABBAS ALLAH YA ISA!!!.

Bari kuji wani hukuncin Allah, ko minti uku banyi ba, sai naga taron mutane akan titi anata zuwa dubawa, nima banyi ƙasa a guiwa ba sai na leƙa, iko sai Allah, mai motar da ya buge mai rake ne kwance ana yi masa fifita gaban motar ya tashi daga aiki, hannunsa ya karye, wai ashe dukan wani bangon titi yayi shi kaɗai yayi accident.

Na sake kallonsa, ya shaidani na shaida shi nace sannu Malam Allah ya kiyaye gaba, TABBAS ALLAH DA ISA YAKE, nayi gaba abina inata tunanin ƘUDIRAR UBANGIJI.

Yakamata muji tsoron Allah mu daina raina kalmar ALLAH YA ISA.

Wani mutumin da ka raina bakasan matsayinsa a gurin Allah ba, sannan bakasan kowanene ba, kowanne mutum da irin baiwar da Allah yayi masa, kowanne mutum yana da wata baiwa wacce kai baka da ita.

Ubangiji ya tsaremu da sharri.

–Sani Rogo Aikawa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button