LABARAI/NEWS

Tambayoyi Zuwa Ga Hukumar NDLEA Akan Zargin Da Take Yi Wa DCP Abba Kyari

Tambayoyi Zuwa Ga Hukumar NDLEA Akan Zargin Da Take Yi Wa DCP Abba Kyari

Daga Datti Assalafiy

Ya kamata duk wani mai hankali da nutsuwa a Nigeria ya tsaya yai tunani da tambayoyi akan abinda ke wakana tsakanin DCP Abba Kyari da hukumar NDLEA, tambayoyi kamar haka:

(1) Me yasa hukumar NDLEA ta boye jami’anta da suke ENUGU wanda sune suke karban kudi daga hannun manyan dilolin hodar iblis suna barinsu suna wucewa sai ‘yan sandan IRT ne suka kama masu safaran kwayoyin?

(2) Me yasa hukumar NDLEA ta roki kotu akan tayi shari’ar mutane biyu da aka kama wadanda suka shigo da hodar iblis daga Kasar Brazil zuwa Ethiopia zuwa Nigeria ta filin jirgin Enugu jami’an sandan na IRT suka kamasu, sukayi transfer case din zuwa ga NDLEA, sai NDLEA tace wai yaran Abba Kyari na IRT sun boye wani kaso na hodar, kuma NDLEA ta roki kotu tayi shari’ar mutane biyun a sirrance don a yanke musu hukunci su tafi gidan yari ba tare da NDLEA ta bari a musu tambayoyi a gaban ‘yan jarida cikin kotu ba?

(3) Sannan idan NDLEA ta taki gaskiya ta fada mana sunan mutum guda daya da take zargi da safaran miyagun kwayoyi da ta taba zuwa ta kama gidansa da gidan iyayensa da gidan kannensa da shagunan kannensa?

(4) Me yasa NDLEA sai akan Abba Kyari ne suka fara kame gida da na iyayensa da na kannensa har ma da shagunan da kannensa suke kasuwanci akan laifin da sun fi kowa sanin cewa bai aikata ba, shin ba sunyi hakane don su boye mummunan cin amanar da jami’ansu na NDLEA da suke ENUGU suke aikatawa ta hanyar karban kudi suna bari ana shigowa da miyagun kwayoyi daga Turai cikin Nigeria ba?

(5) Me yasa NDLEA ba ta shaida wa duniya cewa ‘yan sandan IRT sun kama masu safaran kwayoyi sun kawo musu ba, ina jami’an NDLEA suke sai ‘yan sanda ne zasu yi aikinsu? shin sun tsaya karban cin hanci a gurin masu safaran kwayoyi ko? shin saboda NDLEA su boye gaskiya sai suka juya suka kulla mummunan sharri da makirci akan mutanen da suka muku aiki don kar asirin maciya amana dake cikinku ya tonu ko?

(6) Tun bayan da NDLEA ta shirya zargi akan Abba Kyari, kuma ta hana kotu ta bada belinsa akan laifin da bai aikata ba, zargi ne, bayan case din Abba Kyari, NDLEA ta kama manyan dilolin miyagun kwayoyi a kalla guda 5 zuwa 6 kuma duk ta bari an bada belinsu akan case dinsu wanda yafi na Abba Kyari girma, me yasa NDLEA ta haramta wa Abba Kyari beli amma ta bada belin wasu? shin NDLEA na jin tsoron kada asirin yaransu dake ENUGU ya tonu ne idan Abba Kyari ya samu ‘yanci?

(7) Buba Marwa ya kamata duk wani mai hankali ya tambayeka, shin wani drug dealer ne ka taba zuwa ka kama gidajensa da na iyayensa da na kannensa a Nigeria? ka fito ka fadawa duniya mutum daya da ka taba yiwa haka idan ka taki gaskiya? me yasa sai Abba Kyari ne kadai zaku yiwa haka? kuma mai yasa baku kama gidajen sauran ‘yan sandan da kuke zargi ba sai Abba Kyari kadai, shin kuna da wani personal interest a kanshi ne don yaransa na IRT sun kama masu safaran hodar iblis bayan yaranku da suke ENUGU sun kyale su sun wuce?

(8) Buba Marwa idan bincike na gaskiya da tsakani da Allah kake ta hannun yaronka Sunday Zirandi wanda yaci amanar Abba Kyari, to ba shakka jami’anka da suke aiki a ENUGU su zaka fara kamawa, tunda sune suke bari ana wucewa da daruruwan kilo na hodar iblis suna karban kudi, tunda wadancan drug dealers da yaran Abba Kyari suka kama sun ambaci sunayen yaranka dake aiki a Enugu cewa sune suke barinsu suna wuce idan sun shigo da hodar iblis daga Turai, masu gidansu suna daukarsu a hoto su turawa jami’an NDLEA dake aiki a filin jirgin ENUGU domin a barsu su wuce da hodar iblis ba tare da wani dogon bincike ba, me yasa bakwa son jama’a su san gaskiyar wannan abin?, sai kuka koma kuna ta yada karya da sharri akan ‘yan sandan da suka taimaka suka kama masu safaran hodar iblis suka kawo muku?

(9) Me yasa NDLEA ta sake fitar da wani rahoto na karya da kanzon kurege cewa ta kama wani babban attajirin dan kasuwa ya shigo da kwantena biyu cike da kwayar TRAMADOL wanda kudin kwayar ya haura Naira Biliyan 22, kuma wai yana da alaka da yaran Abba Kyari na IRT Lagos lokacin da suka kamashi sun karbi wani kaso na Tramadol din, idan wannan rahoto na NDLEA gaskiya ne to don girman Allah su bayyana mutumin tare da Tramadol din da sukace sun kama a gurinsa da cikakken alakarsa da Abba Kyari?

(10) Buba Marwa ka tambayi yaronka Sunday Zirandi laifin me DCP Abba Kyari ya masa yake ta bibiyansa da sharri da makirci haka? ko kuma shin yana da wata alaka tsakaninsa da jami’an NDLEA da suke aiki a ENUGU ne?

(11) Jaridu kamar Punch sun ruwaito Labari sukace daga NDLEA wai hukumar NDLEA tace ta gano kudi a cikin account na Abba Kyari kusan Naira Biliyan 1.8 hakanan ta gano kudi a account na Mataimakin Abba Kyari kusan Naira Biliyan 2.6 billion, muna tambayar hukumar NDLEA don Allah ta fitar da Bank account balance na Abba Kyari da mataimakinsa su nuna wa duniya ina kudin suke? domin duk bincike da masu aiki a banki sukayi ya nuna karyane, irin wannan kudi basu taba shiga account na Abba Kyari da mataimakinsa ba,
idan ba haka ba hukumar NDLEA ta fito ta karyata rahoton Punch tare da daukar matakin doka a kan Punch da suka yada labarin karya suka jingina labarin daga NDLEA.

(12) NDLEA tace wai DCP Abba Kyari ya taba yin case din Tramadol na kimanin Kudi Naira Biliyan 3, wannan labarin ma karya ne, NDLEA ta fito ta nuna mana inda haka ya faru, a ina ne akayi case din da Abba Kyari? NDLEA ta fito tayi cikakken bayani akan wannan idan tana da gaskiya, team na IRT reshen jihar Lagos sune suka taba yin case din daga farko har karshe, kuma duk bincike ya nuna babu laifin Abba Kyari a cikin case din, amma sai kuma yanzu NDLEA tazo tana kokarin alakanta case din da Abba Kyari, suka fitar da hoton mutumin da suke zargi hade da hoton Abba Kyari maimakon hoton yaransa na Lagos.

Asalin case din da NDLEA take zargin DCP Abba Kyari bai san lokacin da yaransa suka kama masu safaran hodar iblis din ba a ENUGU, kuma bai san lokacin da aka kammala binciken ba saboda an dakatar dashi daga aiki a lokacin da abin ya faru, to sai a karshen case din lokacin da aka kirashi domin ya taimaka a biya informer tukwicin bada bayanan sirri da yayi kamar yadda aka masa alkawari, akan haka ne sai ya tuntubi SUNDAY ZIRANDI wanda shi babban jami’i ne a hukumar NDLEA kuma Abba Kyari ya yadda da shi a rashin sani, shiyasa ya tuntubeshi domin a biya dan leken asiri hakkinsa.

Kuma shi Sunday Zirandi shine ya tsarawa Abba Kyari duk abinda ya kamata ayi domin a biya Informer hakkinsa, Sunday Zirandi zai iya gayawa Abba Kyari gaskiya akan ko zai yiwu a taimaka a biya informer hakkinsa ko ba zai yiwu ba, amma saboda tsabagen cin amana da yunkurin boye gaskiya sai Sunday Zirandi ya shirya wa Abba Kyari wannan mummunan makirci, kuma yake mika labarun karya ga jaridu irinsu Punch suna ta yada labarin karya da sharri akan Abba Kyari.

Muna amfani da wannan damar wajen kira ga Gwamnatin Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya, muna kira ga Maigirma Ministan Shari’ah kuma babban Lauyan Gwamnatin tarayyar Nigeria Barr Abubakar Malami SAN, a babi na gaskiya da adalci, ya kamata Gwamnatin tarayyar Nigeria ta kafa kwamiti mai zaman kansa akan wannan case din da NDLEA take da Abba Kyari.

Ba shakka akwai alamun gaskiyar da NDLEA take boyewa masu tarin yawa, bisa kwararan hujjoji da dalilai akwai bukatar kafa kwamitin bincike na musamman, a cire hannun NDLEA da Police a cikin binciken, a bawa wata hukumar bincike na dabam kamar DSS ko NIA su jagoranci binciken, sannan ayi gaggawa kama jami’an NDLEA da suke aiki a filin jirgin ENUGU, domin mafi yawan hodar iblis da ake shigowa da ita Nigeria ta hannunsu ake wucewa da shi suna karban kudi daga manyan dilolin hodar iblis kamar yadda drug dealers da ‘yan sandan IRT suka kama suka tabbatar.

Shugaban hukumar NDLEA Buba Marwa ya cancanci a kyautata masa zato na alheri, abin fahimta ga masu ha Mali shine Sunday Zirandi yana bawa Buba Marwa rahoto na karya da ha’inci da makirci yana zama a kai ba tare da ya fahimci boyayyar manufarsa ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button