ylliX - Online Advertising Network Tashin Hankali Yayin da Wani Hadari Ya Lakume Rayukan Mutane Sama da 10 a Bauchi - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Tashin Hankali Yayin da Wani Hadari Ya Lakume Rayukan Mutane Sama da 10 a Bauchi

Tashin Hankali Yayin da Wani Hadari Ya Lakume Rayukan Mutane Sama da 10 a Bauchi

Wani Ibtila’i ya auku a kauyen Hawan Jaki da ke Titin Alkaleri-Gombe a ƙaramar hukumar Alkaleri, jihar Bauchi ranar Asabar yayin da mutane 11 suka mutu a haɗarin mota.

Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra (FRSC) na yankin Bauchi, Mista Yusuf Abdullahi, ya shaida wa hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) cewa wasu mutum 8 sun jikkata sakamakon haɗarin.

Yace hatsarin ya rutsa da wata Motar haya ta kamfanin Yankari Express da kuma wata Motar Ɗangote Mista Abdullahi ya jingina musabbabin abinda ya jawo hatsarin da mummunna tuƙi mai haɗari, inda yace:

Maza matasa 20 ne mummunan haɗarin ya rutsa da su, mutum Tara daga ciki suka mutu nan take a wurin yayin da Likitoci suka tabbatar da cikawar wasu biyu a babban Asibitin Alkaleri.

Haka nan wasu mutum Takwas sun ji raunuka iri daban-daban kuma yanzu haka suna kwance a Asibitin Alkaleri ana kulawa da lafiyarsu. Jami’ai sun kai gawarwakin wadanda suka Mutu asibitin.

Kwamadan FRSC, Mista Abdullahi, ya kara da gargaɗin matafiya cewa a ko da yaushe su rika kokarin kiyayen ƙa’idoji da dokokin tuki yayin da suka hau kan titi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button