LABARAI/NEWS

Tashin Hausawa a kasuwar Alaba Rago dake Lagos ainihin abun dake faruwa kuma na ganewa idona~ Kwankwaso.

Tashin Hausawa a kasuwar Alaba Rago dake Lagos ainihin abun dake faruwa kuma na ganewa idona~ Kwankwaso.

Da farko dai nayi bincike ankuma kawo mun dukkan takardun na gani, ita wannan kasuwar tun lokacin marigayi Murtala Muhammad aka kafata sannan aka rabata zuwa gida uku aka ba inyamurai tasu, sannan akaba yarabawa tasu sannan akaba Hausawa tasu, to yau da gobe yarabawa da inyamurai sun gina tasu ginin zamani tamu ta Hausawa ne sabida wasu dalilai da kuma yanayin mutanen mu yasanya ba agina ba, sai dai ma wasun mu dasu samu dama suke ganin su sun gyara wajansu to shikenan yanzu babu ruwan su da abun da ya shafi wadanda basuyi ƙarfi ba, sai kuma matsala ta biyu da take damun mutanen mu Hausawa itane Ilimi musamman na zamani ina takaici matuƙa naga yaran mu basuyi karatu ba, shiyasa nake iyakar ƙoƙari na kuma duk wanda wata mu’amala ta haɗani dashi babban shawarar da nake fara bashi itane yasa yaransa suyi karatu kai idan ta kama ko sayar da gona ayi suyi karatu, yanzu haka babbar illar datake niyar samun mutanen mu Hausawa a babban kasuwar Legas ɗin rashin wadatuwar karatu yana daga cikin abun daya janyo, sannan gwamnatin Legas tace ta bincika ta gano miyagun mutane na samun mafaka a kasuwar tare da muggan makamai nasa anbincika mun na kuma yi binciken da kaina maganar gaskiya sharri ne da ƙage ga Mutanen mu wannan maganar ba gaskiya bane, kasan yanzu idanun gwamnoni ya rufe kawai su ya zasu ƙwaci filaye su samu kuɗaɗe kawai shine shiyasa suke ƙagar wasu dalilai da suke ganin zasu iya fakewa dasu.

Yanzu dai ka gani mutanen mu na Arewa za’a tasa inyamurai da yarabawa sunanan to akwai laifin mutanen mu kamar yadda na faɗa tun da farko da muma muna da haɗin kai muntsaya mun gina tamu kamar yadda sukayi da hakan bata faru ba.

Babban abun da nake buƙatar gwamnatin Legas tayi anan shine adalci kasan mutun da jahar sa, ina buƙatar tunda ance sabunta ta za’ayi to gwamnati ta biya mutanen mu diyyar kadarori da shagunan su daza ta rusa sannan ta nemo wani guri a kusa daza su koma suci gaba da aiwatar da kasuwancin su, amma akwai mutanen mu da da yawa wasu ma kakanin su can suke acan aka haife su kuma nan ne wajan cin abincin su ba adalci bane atashe su ba tare da ansamar masu wani waje ba, to dare ɗaya ka rushe masu kasuwar ina zasu je?. Wani sashi daga cikin bayanan ɗan taƙarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso a firar sa da gidan rediyon Muryar Amurka VOA Hausa.

Rahoton Khalid Ikara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button