Latest Hausa Novels

TASIRIN DEWORMING TABLET WAJEN WANKE DATTIN CIKI

TASIRIN DEWORMING TABLET WAJEN WANKE DATTIN CIKI

Deworming tablets magunguna ne rukunin Anti helmenthics wato magungunan dake aiki wajan kawar da tsutsotsi, kwayayen tsutsotsin, da kuma macijin ciki tare da dangogin worms ga manya da yara…. musamman a kananun yaran mu.

DEWORMING tablet sun kunshi; ALBENDAZOLE, mebendazole, praziquantel da kuma ivermectin. Sai de a yanzu ko ina dangane da dattin ciki ALBENDAZOLE (zentel) shine yai shura, shi ake recommending ga kowa saboda shine matsayin kamar gangaran wato BROAD SPECTRUM ANTI HELMENTHIS

⚘⚘⚘
Yaran mu sunfi mu kusa da kamuwa da irin wadannan nau’ikan kwayoyin cuta saboda komi suka samu daduma abaki kurum suke walau hannunsu awanke yake koba a wanke ba su ba ruwansu.

Haka ma ta hanyar ta’amalinsu da kayan wasansu wasu yaran haka zakaga sun dau takalmi ma sun duma abaki suna tsotsa ba ruwansu wanda kuma su irin wadannan kwayoyin cuta a kasa dama ake samun su… sai sun shiga ciki suke kyankyashe kansu su haddasa matsala.

⚘⚘

Abune mai mahimmanci baiwa yaran mu da kannen mu tare damu kanmu kwayar maganin tsutsar ciki, micijin ciki da dattin ciki wato [ALBENDAZOLE] kamar yadda wasu kan kirasa da ZENTEL

Lallai ka/ki ke ba yaranku duk bayan watanni 3 ko 6 saboda ya kashe kwayoyin tsutsa din dana fada.

Saboda irin wadancan kwayoyin cuta suke:

■ Su ke daqile saurin girman yara,
■ Su kansa yaro yawan kashi baji bagani
■ Su kesa ganin tsutsotsin ciki
■ Su kesa ake ganin macijin ciki kuru-quru acikin kashin mutum
■ Yawan tara miyau abaki musamman a manya ko dalalar miyau a yara

■ Su kesa aga yara suna fitar baya wato insun gama kashi anzo wanke musu aga duburarsu ta burtso sai an matse duwawunsu ta koma….

■Sukesa mutum saurin jin yunwa nan da nan inyaro ne aga yafiye ci kamar me… har kuka yake duk da bai jima da gama cin abinci ba… saboda tsutsotsin ke tsotse abunda yaci

■ Su kuma ke haifar ma yara karancin sinadarin “IRON” wanda ke Samar da wadataccen jini,

Wannan tasa wasu yaran ke tsumburewa alhalin suna da mugun cin abinci Amma kaga Basa Kumari, Saboda yara kan hadu da irin wannan kwayoyin kamar yadda na fada abaya wajen wasan kasa, wasa da kwata, shan ruwan rafi, tare da cin abinci bayan tabe-tabe batare da hannu ya wanku sosai ba.

Albendazole din kadai duk ya isa yakau da wadancen tarin abubuwan da kwayoyin cutar ke haddasawa

⚘⚘⚘
LIKITA YA MAGANIN YAKE?

Albendazole kanzo a 400MG duk kwaya daya a wanda yake zuwa a farar robar magani kenan wato na tsaba ko ince dan Qirga, HAKA kuma idan dan kwali ne yakan zo a 200MG Amma kwaya biyu ne a kwalin kunga ya tashi a 400MG kenan total.

Sannan akwai na ruwa na yara yan sama da shekara daya duk da ana iya basu na Kwayar, shima na ruwan akwai yar robar bayarwa 2.5ml acikin kwalin

Kowanne ne de ya samu za’a badashi ne daidai da shekarun mutum…. kuma sau 1 tak sai bayan wasu watanni uku din… saide in ayanzu already ansan yaro na da daya daga cikin matsalolin dana lissafa toh shine sai abashi sau 1 kullum na tsawon kwana 3 ajere shikenan. Sai bayan wata 3 abashi sau 1.

LIKITA ME ZA’A KAUCEWA GAME DASHI

■ Maganin de in na kwaya ne ana tauna shi ahadiye ne Saboda baida d’aci, sai zaqi ma da yake dashi. Ba’a son a hadiyesa da ruwa sai abayan antauna an hadiye sai abi da ruwa.

■ Anso kar aba yaro sai wanda yai shekaru biyu cif cif watanni “24” amma idan yaro kafin yakai shekarun akaga ya nuna alamun kwayoyin cutar to inde ya shekara toh a iya bashi… amma wanda baici shekara 1 a duniya ba sam kar a kuskura abashi

■ Me shayarwa zata iya sha musamman in dan yakai wata 6 a duniya ba matsala. Inkuma ya gaza wata 6 amma de gashi tana da matsalar nan ma zata iya sha saide anso kar yaron yai kasa da wata 6 saboda yana bin nono ya shiga cikin yaron… kila yasa shi gudawa.

■ Haka mace me mai juna biyu bata sha SAIDE IN TANA DA MATSALAR kuma babu wani za6i sai shi toh ana iya basu su sha sau 1 shikenan ba wani illah insha Allahu

⚘⚘⚘
YADDA AKE BAYARWA SHINE

Anso asha sa da daddare yayin kwanciya bacci saboda ciki zamo empty a lokacin… basai anci abinci ba, infact yafi tasiri a empty stomach

■ Idan shekarar yaro 1 bukata ta tashi toh za’a 6alla guda 1 gida biyu abashi rabi idan na kwaya ne me 200MG, idan kuwa me 400MG ne za’a 6alla 4 sai abashi kaso daya… wato de 100MG kenan

■ Idan ya shekara 2 za’a 6alla guda mai 400MG abashi rabi, kunga yasha 200MG kenan.
In kuwa dan kwali ne dama a 200MG yazo guda biyu kunga kai tsaye sai abashi guda daya ya tauna ya hadiye wato 200MG shikenan sai Kuma bayan wasu watanni ukun.

■ Amma daga yan shekara 3 zuwa 12 za’a iya basu guda guda wato 400MG din duka su tauna su hadiye

■ Manyan kuma daga shekara 13 zuwa sama zasu iya shan kwaya biyu wato 800MG.

⚘⚘⚘

WANI KARIN HASKE

Musamman a manya wadanda keda tsutsar ciki ko macijin ciki nakan bada shawara kafin susha da minti 15 ka sami ayaba ko gyada, ko kuli-kuli kaci inyaso bayan kamar minti 15 sai ka tauna maganin inka hadiye sai kabi da ruwa, hakan zai zamo kamar tarko inda maganin zai sami tsutsotsin guri guda ya kashe.

RASHIN BIN KA’IDA

Yana iya sa gudawa kadan ko me dan yawa wato idan dadinsa yasa yaro ya haike masa yace zaita sha, musamman ace yasha kwaya 5 lokaci yini guda

Amma baya kisa bakuma ya sanya Amai

FATAN MUN ILMANTU

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button