Tirkashi : Amal Umar tagito karara ta bayyana rashin amincewar kan barin ya’ya mata shiga harkar kannywood

Amal Umar ta bayyana rashin amincewar ta kan barin ya’ya mata shiga harkar fina finai kannywood bisa wasu dalilai data zayyana
Amal dai ta bayyana Hakan me a wani fefan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta inda ta nuna illar barin ya’ya mata shiga harkar fina finai musamman ayanzu da harkar tazama abunda ta zama
Harkar dai ta fina finan hausa na cigaba da Shan suka musamman ganin yadda jaruman ke aikata abubuwa rashin tarbiyya a shafukan sada zumunta
Ko a baya bayan Nan am hango wani fefan bidiyon tsaraici wata jarumar kannywood din lamarin da yayi sanadiyyar korar ta daga masana’antar ta kannywood
Haka Kuma yadda jaruman kannywood din Hadi da mawakan cikin masana’antar ke yin Wakokin rashin tarbiyya da Kuma yadda abubuwa badala yayi yawa a cikin masana’antar
Wannan yasa jarumar Amal Umar ta bayyana ra’ayin ta kan barin ya’ya mata shiga harkar kannywood inda tace gaskiya yanzu akwai matsala babban a barin ya’ya mata shiga film