Tirkashi anata cece kuce kan irin abinda jarumi Tahir Fagge yayi a Gidan Gala

Tirkashi anata cece kuce kan irin abinda jarumi Tahir Fagge yayi a Gidan Gala
Daya daga cikin jaruman masana’antar Kannywood iyaye kuma wato Tahir fagge kenan yake tikar rawa acikin wani faifan bidiyon sa da aka sake.
Wannan bidiyon yasa mutane sunata kara fadin abubuwa marasa dadi akan masana’antar Kannywood domin kuwa mutane suna bayyana cewar dama ba fadakarwa sukeyi ba illa lalata tarbiya acewar mutane.
Cikin faifan bidiyon dai jarumin shida wata budurwa awani gidan gala inda suke rera wata tsohuwar wakar hausa maisuna “bazar kowa bazar kowa da bazarki nake taka rawa, da bazarki ninake taka rawa”
Wannan bidiyon jarumin ya matukar janyo cece kuce domin ana ganin Tahir Fagge a matsayin uba acikin masana’antar Kannywood baikamata ace yana irin abubuwan da kananan yara sukeyi ba, haka zalika mutane sunata nuna rashin jin dadinsu dangane da wannan lamarin.
Ga video