Tirkashi wasu batutuwa akan kama murja yar Tiktok

Tun bayan da aka kama shahararriyar yar Tiktok murna kunya , al umma da dama na cigaba bada tofa albarkacin bakin su kan wanna batu
Yan sanda a jihar Kano dai sun cafke murja ne a lokacin da ake daf da gudanar da shagalin murnar ranar haihuwar ta a wani babban hotel
Murja wacce ke hannun yan sanda na cigaba da amsa tambayoyin akan abubuwan da ake zargin ta wanda suka haÉ—ar da zage zage a kafar Tiktok
Ana dai tuhumar murja kunya da zage zage, tare da ciwa mutane mutunci a shafukan sada zumunta wanda ya sanya yan sanda suka kama ta
Wannan dai ba shine karon farko da hukumar yan sanda sukayi kokarin kama wannan yar Tiktok ba , sunan murja dai na cikin jerin sunayen da aka aikewa da gomnan Kano bisa zargin su da bata tarbiyya
Hakan ya sanya yan sanda bayyana kana su sai dai kuma murja tare da sauran wanda aka bada umarnin kana su suka tsere daga jihar Kano