ylliX - Online Advertising Network TSAKANIN KUNGIYAR BOKO HARAM DA ISIS za'a yiAuren Zobe - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

TSAKANIN KUNGIYAR BOKO HARAM DA ISIS za’a yiAuren Zobe

TSAKANIN KUNGIYAR BOKO HARAM DA ISIS za’a yi
Auren Zobe

Haƙiƙanin sunan Kungiyar Boko Haram shi ne Jama’atu Ahlus sunnah Lidda’awath wal-jihad amman an fi saninsu da sunansu,

Yan Boko Haram Kungiya ce ta ‘yan jihadi da ke da cibiyarta a Birnin Maiduguri, na jihar Borno a Arewa maso gabashin Nijeriya. Suna adawa ne da dokokin da ba na Allah ba da kuma kimiyyar Zamani.

A shekara ta 2002 wani mutum da ake kira da Muhammad Yusuf ya kirkiri kungiyar kuma suke son tabbatar da Shari’ar Musulunci a Nijeriya. Hakazalika, kungiyar Boko Haram ta yi kaurin suna kan kaiwa jami’an hukumomin tsaro da ma’aikatun gwamnati hare-hare da dasa bama-bamai a wuraren taruwar jama’a mabambanta.

Tun daga shekarar 2009 hukumomi a Nijeriya suke yaƙi da ƙungiyar ta Boko Haram wadda ta yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da lalata dukiya ta miliyoyin nairori.

Rikicin wanda aka faro a jihar Borno da ke arewa maso gabas ya fantsama zuwa makwabtan ƙasashe kamar su Nijar da Chadi da kuma Kamaru.

A watan Afrilun shekarar 2014, Boko Haram ta sace ‘yan mata 276 ‘yan makaranta daga Chibok. wanda Shekau ya sanar cewa zai saida su a matsayin bayi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button