ylliX - Online Advertising Network Tsaro: A kwantar da hankula, Buhari ya shawarci ƴan Nijeriya - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Tsaro: A kwantar da hankula, Buhari ya shawarci ƴan Nijeriya

Tsaro: A kwantar da hankula, Buhari ya shawarci ƴan Nijeriya

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya shawarci hukumoin tsaron ƙasar da dukkan al’umma da su ci gaba da yin taka-tsantsan da kula da sha’anin tsaro, amma kuma ya ce ya na da matuƙar muhimmanci a guji tayar da hankula.

a wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar a yau Juma’a, shugaban ya nemi ƴan ƙasar da su kwantar da hankali. “Sabbin matakan barin ƙasar da Amurka da Birtaniya ke ɗauka ba za su zama dalilan tayar da hankali ba

Wannan magana ta shugaban ƙasar na zuwa ne a yayin da hankula ke ci gaba da tashi kan batun tsaro a Najeriya, tun bayan gargaɗin da Amurka da wasu ƙasashen yamma suka yi cewa akwai yiwuwar kai hare-haren ta’addanci a ƙasar.

Najeriya ba ita kaɗai ce ƙasashen duniya ke bai yi wa gargadi kan barazanar ta’addanci da kuma bai wa ƴan ƙasashensu shawarar tafiye-tafiye ba.

Amurka da Birtaniya na kuma yin gargaɗi kan yiwuwar hare-hare a ƙasashen yammacin Turai. Sannan sun bai wa ƴan ƙasarsu irin shawarwarin da suka fitar a Najeriyar.

Abin takaici ne cewa batun ta’addanci ya mamaye duniya Sanarwar ta ci gaba da cewa sai dai gargaɗin ba yana nufin lallai za a kai hare-haren ba, don tun bayan harin da aka kai gidan yarin Kuje an sake tsaurara tsaro a ciki da wajen Abuja.

An daƙile hare-hare. Jami’an tsaro ne bankaɗo barazanar da ake fuskanta don tsaron ƴan ƙasa – sai dai mafi yawan ayyukansu ba a gani saboda ana buƙatar sirri.

Zaman lafiyar ƴan Najeriya shi ne mafi ƙololuwar burin gwamnati. Jami’an tsaro na aiki babu dare babu rana,” in ji sanarwar.

Kazalika shugaban ƙasar ya bayar da tabbacin cewa gwamnati na bakin ƙoƙarinta wajen tabbatar da tsaro.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button